Connect with us

Hi, what are you looking for?

Kotu

Kotu Ta Rufe Asusun Hisbah A kano, Bisa Ƙin Biyan N800,000 Ga Masu Otel

Hisbah
Hisbah

Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta ce an rufe dukkan asusunta na banki bayan ƙarar da masu otal din suka shigar kan hukumar.

Kwamandan Hisbah, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa, ya tabbatar da hakan ga kafar yaɗa labarai ta TRT Afrika Hausa a ranar Laraba.

Idan za a iya tunawa, watannin da suka gabata ne jami’an Hisbah suka kai samame a wasu otel-otel da wuraren nishadi a Kano lamarin da ya haifar da taƙaddama.
Daurawa ya ce, “Eh, gaskiya ne an kulle dukkan asusunmu na banki. Na tura wakili don ganawa da Babban Lauyan Gwamnati saboda ba a gaya mana game da laifin da ake zargi da kuma dalilin rufe asusun ba.

“Mun samu takardar kotu da ke zargin wai ma’aikatan hisbah sun yi musu ɓarna a lokacin da suka je gudanar da aikin su a wasu otal guda biyu, wanda hakan ya haifar da tuhumar N700,000 da N100,000 bi da bi. Takardar ta bukaci a hada biyan naira 800,000, wanda hakan ya sa aka rufe asusunmu.

“Ya kamata a gaya mana game da laifin da muka aikata domin mu nemi lauyoyinmu su shiga cikin tattaunawar. Idan muka gaza kare kanmu, to, za a yi mana hukunci.

Daurawa ya kuma nuna damuwar cewa hukuncin kotun ya gurgunta ayyukan Hisbah saboda garƙame bakin asusun bankin.

STENTORNEWS, ta tuntuɓi Darkatan Wayar da kan Al’umma na hukumar Hisbah, Auwalu Ado Sheshe, domin karin haske ga wannan turka-turka, ya ce “wannan maganar tsohuwa ce domin ta kai shekara biyar da yin ta, sai yanzu ƙungiyar masu otel suka sake bujiro da ita.
Mu muna ganin hakan ƴana da nasaba da wasu waɗan da ke ƙiyaya da hukumar ta hisbah, kuma insha Allahu an kusa a warware matsalar”, inji Darktan

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You May Also Like

Lafiya

Daga Dr. Sunusi U. Na’ibi Yadda mutum ke wanke baki da kuma irin burushin da yake amfani da shi suna iya canza lafiyar baki...

Noma da Kiwo

DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA (2) Daga Yazid Sunusi YahayaRead also: DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA UKU (3)...

Noma da Kiwo

Dabarun kiwan kaji a lokacin yanayi na sanyi Daga Yazid Sunusi YahayaRead also: DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA UKU (3) Sau...

Kano

Gwamnatin Kano Ta ƘirƘiri Sabon Tsarin Biyan Fansho da Giratuti Ta Intanet Gwamnatin Jihar Kano ta ƙaddamar da wani sabon tsari na musamman na...