Hukumar Hisbah ta jihar Kano na kara jaddada kudurinta na hada kai da ƙungiyoyi masu zaman kansu domin wayar da kan al’umma kan annobar cutar HIV/AIDS da kuma inganta rayuwar mata da matasa.
A cewar ofishin hulɗa da jama’a na hisbah, Lawan Ibrahim Fagge ya ce Darakta Janar na Hukumar, (DG) Alhaji Abba Sa’id Sufi, ne ya bayyana hakan a lokacin da yake ganawa da Babban Jami’in Kula da Harkokin Kiwon Lafiya na Mata (WHEI), wanda ya ziyarci shedikwatar Hukumar Hisbah.
Read also: Hukumar Shari’a da Rundunar Yan sanda a Kano za su kawo karshen faɗan daba da kwacen waya
Alhaji Abba Sa’id Sufi ya bayyana cewa ya zama wajibi hukumar ta tallafa wa duk wani shiri da ƙungiyoyi masu zaman kansu suka yi wanda ya dace da koyarwar addinin Musulunci da kuma taimakawa wajen inganta yanayin kiwon lafiyar al’umma a jihar.
Read also: Wasu Ma’aikatun Gwamnati Zasu Sami Sabbin Shugabanni A Kano
Tun da farko da take jawabi babbar jami’ar (WHEI) Hajiya Aisha Muhammad Umar ta buƙaci goyon bayan hukumar wajen ci gaba da ƙoƙarin wayar da kan mata da matasa game da cututtuka masu hadari.
Read also: Jami’in KAROTA Yayi Sanadin Kama Wani Da Ake Zargin Barawan Mota da Kuma Kungiyar Su A Kano
Shugaban ya kuma jaddada buƙatar hadin gwiwa wajen yaƙi da cutar HIV/AIDS da kuma inganta lafiyar haihuwa da ‘yanci.
Ta yi nuni da cewa, kamar yadda a halin yanzu WHEI ke samar da ayyukan kiwon lafiya da kayan aiki ga al’ummomin da ke jihohin Kano, Jigawa, da Katsina, akwai bukatar yin hadin gwiwa.




























