Kimanin matuka Baburan a dai-daita sahu guda 100 Hukumar Hisbah tayi holinsu a shalkwatanta da ke unguwar Sharada, waɗanda suka taka dokar sana’ar daukan fasinja a cikin kwaryar birnin kano.
Da yake ƙarin haske a kan matuƙa Baburan a dai-daita sahun, Babban kwamandan hukumar Hisbah, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ya ce daga ciki an sami mutane 24 da laifin cakuɗa maza da mata a baburansu, sai mutane 35 waɗanda suka yi askin banza, mutum 12 sun liƙa hotunan batsa a jikin baburansu, da waɗanda ke sanye da gajerun wanduna mutum 11 da masu ƙure sautin kida ya yin tuƙi da sauransu.
Read also: Wasu Ma’aikatun Gwamnati Zasu Sami Sabbin Shugabanni A Kano
Babban kwamandan Hisbah wanda ya yi magana ta hannun mataimkinsa mai kulla da aiyukan yau da kullum (operations) Dr. Mujahid Aminudeen Abubakar, yace daga yanzu Dakarunsa zasu ci gaba da sa ido domin tsaftace sana’ar a dai-dai ta sahun a jihar kano.
Babban kwamandan hukumar Hisbah yace babban abin takaici, mafirinjaye daga cikin adadin waɗanda dakarunsa suka kamo, ko da aka bukace su da gabatar da rukunan sallah ba su iya ba, daga cikin har da waɗanda suka kasa karanta Fatiha da sura wasu daga cikin surorin Alqur’ani Mai tsarki.
Read also: Hukumar Shari’a ta Yi Wa Wasu Alƙalai da Ma’aikata Ritayar dole A Jihar Kano
Ya shawarci iyaye da sauran jama’a da su dage wajen sauke nauyin da shari’a ta yi ummarci mahaifi ko mahaifiya su yi musaman a kan neman illimin addini da na zamani, domin samar da al’umma mai cike da tarbiya da kyawawan aiki a rayuwa.
Kwamandan hisbah ya ba da umarni ga sashin wayar da kai da na Da’awa da su koyawa waɗanda su ka kasa karanta Fatiha da sura da waɗanda suka gaza kawo rukunan sallah har sai sun iya a matsayin beli, tare da daukan cikakken suna da addireshi da lambar a daidaita sahun.
Read also: One Kano Agenda: Gwamna Yusuf Ya Nuna Samun Haɗin Kai Shine Mabuɗin Farfaɗo da Jihar Kano
A nata jawabin Mataimakiyar Babban kwamandan Hisbah Mai kulla da sashin mata, Dr. Khadija Sagir Sulaiman ta shawarci masu sana”ar tuka Baburan a jihar kano da su ji tsoron Allah kuma su dai na cakuda maza da mata a baburansu domin samun ɗaukaka da arziki mai ɗorewa.
Jami’ian hurɗa da jama ‘a da ƴan jaridu na hukumar hisba Malam Lawan Ibrahim Fagge, ya ruwaito mana cewa Babban jami’in Hisbah Mai kulla da sashin aiyukan yau da kullum, ACG Abubakar Salihu yace Dakarunsu sun gabatar da sumame tare da cafke matuka Baburan a daidaita sahun a kan titin gidan murtala zuwa Jami’ar Bayeeo ta Kano (BuK), da titin Kofar kabuga zuwa Kofar Ruwa da titin kabuga zuwa titin Tal’udu zuwa Asibitin murtala, da titin gidan sarki zuwa Kofar Nassarawa da sauran su.




























