Connect with us

Hi, what are you looking for?

Labarai

Wa’adin  Rufe  Samar Da Biza Na Aikin Hajjin Bana Ranar 29 Ga Afrilu, 2024 Na nan Ba Chanji

DG Danbappa
DG Danbappa

Darakta-Janar na hukumar jin dadin alhazai ta jihar Kano, Alhaji Laminu Rabi’u Danbappa, ya sanar da hakan a ranar Talata a yayin wata liyafar cin abinci da aka shirya don samun nasara a Kotun Ƙoli da Gwamna Kano Abba Yusuf ya samu wanda jami’an kula da aikin Hajji na kananan hukumomi 44 suka shirya.

Alhaji Laminu ya ce masarautar Saudiyya ta ce tana nan kan matsayinta kan dokoki da ka’idojin aikin Hajji na shekarar 2024 da suka tanadar, kamar yadda aka sani an tsayar da ranar 29 ga watan Afrilun 2024 a matsayin wa’adin samun biza ga dukkan maniyyata.

Alhaji Laminu Rabi’u Danbappa ya buƙaci jami’an aikin hajji na Ƙanana hukumomi da su fadakar da jama’a sosai game da wannan wa’adin, don tabbatar da babu wani mahajjaci da aka bari a baya.

Da ya juya kan liyafar karrama Gwamna Alhaji Abba Kabir Yusif, Alhaji Laminu Rabi’u Danbappa ya bayyana cewa, wannan shi ne matakin farko, inda ake sa ran samun ƙarin ci gaba.

Ya yi addu’a ga Allah Madaukakin Sarki da ya yi wa Gwamna Abba Yusuf jagora tare da kare shi a dukkan al’amuransa.

A lokacin da yake gabatar da nasa jawabin, shugaban ƙungiyar masu kula da ayyukan Hajji na Ƙananan hukumomi 44 wanda kuma shi ne jami’in kula da aikin Hajji na ƙaramar hukumar Bichi, Alhaji Habibu Idris Bichi, ya bayyana cewa an shirya liyafar ne domin karrama Gwamna Abba Kabir Yusif bisa nasarar da ya samu a Kotun Ƙoli a kwanan nan.

Alhaji Habibu Idris Bichi, a madadin dukkanin jami’an cibiyar aikin hajji na Ƙananan hukumomi 44, ya yi alkawarin yin ƙoƙari wajen sayar da kujerun Hajji don cimma burin da aka sanya a gaba.

Suleiman A. Dederi jami’en hurɗa da jama’a na ofishin hukumar akin hajji na jihar Kano shi ya bada wannan sanarwa ga manema labarai.

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You May Also Like

Lafiya

Daga Dr. Sunusi U. Na’ibi Yadda mutum ke wanke baki da kuma irin burushin da yake amfani da shi suna iya canza lafiyar baki...

Noma da Kiwo

DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA (2) Daga Yazid Sunusi YahayaRead also: DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA UKU (3)...

Noma da Kiwo

Dabarun kiwan kaji a lokacin yanayi na sanyi Daga Yazid Sunusi YahayaRead also: DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA UKU (3) Sau...

Kano

Gwamnatin Kano Ta ƘirƘiri Sabon Tsarin Biyan Fansho da Giratuti Ta Intanet Gwamnatin Jihar Kano ta ƙaddamar da wani sabon tsari na musamman na...