Jagoran gwamnatin jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya musanta jita-jitar da ake yadawa cewar sun yi fada da Sakataren Gwamnatin Jiha, Dr. Baffa Abdullahi Bichi har ya sa an yi kasa-kasa da shi, wanda shi ne sanadiyyar rashin lafiyar Baffa Bichin.
Gwamnan ya furta haka ne yayin da yake jawabi a gun taron rantsar da sabbin manyan sakatarorin gwamnati guda (21) da masu ba da shawara na musamman guda (14) a gidan gwamnati a ranar Talata.
Read also: Gwamnan Abba Yusuf ya gabatar da kasafin kuɗin 2026, na zambar N1.368 tiriliyan
Gwamnan ya ce babu wata farfaganda da za ta hana gwamnatinsa cimma burinta na kyautata wa jama’ar jihar Kano da ci gaban jihar.
Read also: Gwamnatin Kano Ta Ce Za Ayi Adalci Ga Ɗaliban Da Aka Kashe, ‘Yan Sanda Sun Kama Ɗalibai 11
Abba Kabir Yusuf ya bayyana cewa nadin shugaban ma’aikatan jiha, a matsayin mukaddashin SSG ba yana nufin an kori Baffa Bichi daga mukaminsa ba ne.
Yayin da yake magana kan yada labaran karya suka yadu a jihar, Abba Kabir ya kara da cewa, wadanda suke daukar siyasa a matsayin madogararsu ta rayuwa, su ne suke kirkiro jita-jita don tada hankulan jama’a, amma kuma hakar su ba ta cimma ruwa ba.
Read also: Gwamna Abba Ya Miƙa Sunan Murtala Garo ga Majalisa Domin Sahalewa Ya Zama Mataimakin Sa
Gwamna Yusuf, ya ce “na ba da rikon mukamin ofishi sakataren gwamnati ne saboda muhimmacin da yake da shi, ba zai yiwu a tafiyar da gwamnati ba tare da ofishin ba,” in ji Abba.
Don haka ya tabbatar cewa idan Baffa Bichi ya samu sauki, to da zarar ya dawo zai ci gaba da aikinsa.




























