Allah daya gari ban-bam, kasar Switzerland ta sahale wa al’umar garin fara aiki da na’urar kashe kai batare da samun wata wahala ba a hukumance.
Rahotani sun ce a halin yanzu kasar Switzerland ta amince da mutum zai iya kashe-kansa-da-kansa cikin sauki ba tare da wani tashin hankali ba.
Read also: Motar Dangote Ta Kashe Mace Mai Ciki, Yaro Da Mutum Shida A Ondo
Amadadin mutum ya kashé kansa a gida da wuƙá, ko da igiya, ko ya fáɗo daga bene da makamantan su, yanzu waya kawai zai buga a zo har gida da na’urar a gaban ‘yan uwa da abokan arziki mutum ya mutu nan take, batare da wata wahala ba, bayan an yi bankwana.
Idan za a iya tunawa, ƙasar Switzerland ita ce ƙasa mafi daɗin rayuwa ta zahiri a yanzu haka a Turai, ita ce kuma mafi yawan albashi da kyan yanayi da tsafta da kuma ingantaccen tsaro, duk da haka ‘yan ƙasar sune kan gaba wajen kashé kansu a Duniya.
Read also: Shugaban Burkina Faso ya kori Jami’ar Majalisar Dinkin Duniya Carol daga ƙasar
Masu magana na cewa, “idan dali yai yawa sai mutum ya ce Allah kashe ni’. Allah ya kyauta.
Read also: Fursunoni 61 Sun Haddace Alƙur’ani Mai Tsarki a Gidan Gyaran Hali na Kano
Zangon Labarai




























