Shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu ya ce yana matukar alfahari da salon jagorancin Dr. Abdullahi Umar Ganduje yake nunawa a matsayinsa na shugaban jam’iyyar APC na kasa.
Tinubu ya bayyana haka ne yayin da Dr Abdullahi Umar Ganduje da mambobin kwamitin gudanarwa na jam’iyyar (NWC) suka kai masa ziyara a Legas ranar Alhamis.
Idan za’a iya tunawa Shugaba Tinubu yana gudanar da hutun kirsimeti da na sabuwar shekara a Legas.
Sanarwa hakan ta fito ta hannun Babban mai taimakawa shugaban Jam’iyyar APC na kasa kan harkokin hotunan masu motsi da taruka, Aminu Dahiru.
Tinubu ya ce, “Ina alfahari da shugabancin ku da sabbin tsare-tsare da kuka bullo da su.
Read also: Shugaba Tinubu ya Amince da Ranakun Hutun Sallah Ƙarama

“Ni ma dole in gode muku ta yadda kuka kawo zaman lafiya a jihar Ondo a cikin jam’iyyar.” Inji shugaba Tinubu
Da yake jawabi, Dr Abdullahi Umar Ganduje ya yabawa shugaba Tinubu kan goyon bayan da yake baiwa shugabannin jam’iyyar.
Read also: “Babu Wani Dalilin da Zai Sa Na Yi APC”, Wanna Wasan Fulani Ne da Kanuri – Sule Lamido
Ganduje ya ce, “Mai girma shugaban kasa, dole ne in yaba maka bisa goyon baya da hadin kai ga shugabancin jam’iyyar.
“Alkawarin da kuka yi na ba Najeriya alkibla da kuma dakile tasirin cire tallafin mai ya yi.”




























