Connect with us

Hi, what are you looking for?

Labarai

Diban Kudin Kananan Hukumomi A Gina Gadoji A Birni Kuskure ne, Gwamnati ta sake Lale – Abba Hikima

Abba Hikima
Abba Hikima

Lauyan nan na Kano, Abba Hikima Fagge, ya bukaci Gwamnatin Kano da ta duba Allah ta tsayar da aikin gadojin da ta kuduri aniyar yi a Kano ta hanyar ɗibar kudaden kananan hukumomi don gina gadoji a birni alhali kauyuka na cikin matsanancin hali da bukatar aiki.

Abba Hikima ya bayana hakan a shafinsa na Facebook a safiyar ranar Laraba dai-dai da lokacin da Gwamnatin Abba ta sanya harshashin ginin gadoji guda biya a cikin birni.

Hikima ya ce, “Irin wadannan abubuwan da ake dauko wa ke sawa mutane suke wa gaba dayan ‘yan siyasa kudin goro, wato irinsu daya, ”

Abba Fagge, ya ce Kuskure ne babba kuma bai Kamata Gwamnatin Jihar Kano ta dauki Kuɗaɗen Ƙananan Hukumomi ta gina gadoji a birni ba, bayan ga tarun bukatun aiyuka raya kasa da ake bukata a karkara.

“Yanzu saboda Allah ina adalci anan? Kauyukan Kano suna cikin mugun hali, kwanaki Freedom Radio ta yi ta bankado matsalolin kauyukanmu amma a dauko kudinsu a saka a gada guda daya me wannan kudin?”

“Lallai akwai wani abu da yake faruwa a kasa.” cewar Abba Hikima.

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You May Also Like

Lafiya

Daga Dr. Sunusi U. Na’ibi Yadda mutum ke wanke baki da kuma irin burushin da yake amfani da shi suna iya canza lafiyar baki...

Noma da Kiwo

DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA (2) Daga Yazid Sunusi YahayaRead also: DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA UKU (3)...

Noma da Kiwo

Dabarun kiwan kaji a lokacin yanayi na sanyi Daga Yazid Sunusi YahayaRead also: DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA UKU (3) Sau...

Kano

Gwamnatin Kano Ta ƘirƘiri Sabon Tsarin Biyan Fansho da Giratuti Ta Intanet Gwamnatin Jihar Kano ta ƙaddamar da wani sabon tsari na musamman na...