Daga Abdu Ado
Babbar Kotun Tarayya da ke birnin tarayya, Abuja ta haramta wa tsohuwar Ministar Mata da Walwalar Al’umma, Pauline Tallen sake rike wani mukamin gwamnati.
Read also: Ɗan Jarida Zai Gurfanar da Hadimin Gwamna Kano a Kotu, Sakamakon Zargin Cin Zarafi
A wani hukunci da ta yanke a ranar Litinin, kotun ta yi tir da kalaman da tsohuwar ministar da ta yi a shekarar da ta wuce, inda ta caccaki wani hukuncin kotun tarayya da ke Jihar Adamawa.
Kotun da ke zamanta a birnin Yola, babban birnin Adamawa, ta soke cancantar takarar A’ishatu Dahiru Binani ta jam’iyyar APC da ke neman kujerar gwamnan jihar.
Read also: Ingila Za Ta Haramta wa Dalibai Amfani da Wayoyin Hannu a Makarantu
Sai dai Tallen ta nuna rashin gamsuwarta da hukuncin na kotun wanda ta bayyana a matsayin “musgunawa wani bangare na al’umma”, yayin da ta bukaci ‘yan Nijeriya da su yi watsi da hukuncin.
Shugaban lauyoyi na kasa, Yakubu Maikyau ya bukaci Tallen da ta nemi afuwa kan kalamanta, inda har ya yi barazanar maka ta a gaban kuliya.
Sai dai tsohuwar ministar ba ta nuna halin ko-in-kula ba.
Read also: NASIR EL-RUFAI YA NEMI AFUWA KAN KARAR DA ICPC TA SHIGAR A KANSA
LDSHIP



























