Ma’aikatan da aka dakatar daga karbar albashi bayan shudewar gwamnatin Ganduje sun koka wa gwamnatin Abba Kabir Yusuf da ya cika musu alkawari kamar yadda ya tabbatar musu da maido su kan taswirar biyan albashi na jiha.
Ma’aikatan sun koka tare da bayyana korafinsu ta daya daga cikin gidajen radiyo a Jihar Kano.
Idan za a iya tunawa, tun da fari an ce yawan ma’aikatan da aka dauka aiki sun kai dubu 12,566, amma gwmantin Abba Kabir ta kafa kwamiti tare da taza da tsifa, kwamiti ya tantance kimani mutum dubu 9330 tare da ba su tabbacin samun albashi a wata Nuwamba kamar yadda Shugaban Kwamitin tantancewar kuma Sakataren gwamnatin Jihar Kano, Dakta Abdullahi Baffa Bichi ya sanar wa manema labarai, sai dai har yanzu hakan ba ta tabbata ba.
A lokacin Dakta Abdullahi Bichi ya ce gwamnati ta sanya a cikin kwarya-kwaryar kasafin kudi har naira miliyan 507 domin biyan ma’aikatan da aka dawo da albashinsu, sai dai ma’aikatan sun ce har yanzu ba su gani a kasa ba.
Kwamared Abdulrashid Yusuf Adam, shi ne Shugaban Kungiyar Sabbin Ma’aikatan da aka hana albashin, ya ce duk da cewar gwamnati ta ce an dawo da su kan albashin, amma suna tsammani gwamnatin ta cire su daga kan jadawalin tsarin biyan albashin kwata-kwata, domin duk kokarinsu ya gaza wajen bude tasawirar.
Read also: Hukumar Shari’a ta Yi Wa Wasu Alƙalai da Ma’aikata Ritayar dole A Jihar Kano
“Mun dau lokaci tun daga ranar 21 ga watan Nuwamba har zuwa 31 ga wata muna ta dako amma idan muka shiga kan shafin biyan albashin idan muka sa lambar “ID” dinmu sai ya gaggara budewa, kuma a nuna mana cewar wannan lambar an dakatar da ita ga bude jadawalin tsarin biyan albashin.
Mun saurara tare da tunani abin zai samu amma haka ta kasa cimma ruwa duk da mun zata gwamnati tana sane amma har yanzu babu labari kuma mu a zaton mu gwamnati ba ta magana a kan abin da ba ta shirya ba.”
“Don haka mu yanzu murna ta koma ciki, domin ya zuwa yanzu an gaza biyan mu hakkinmu mu duk da aikin da muke zuwa yau kimanin wata 7 kenan babu albashi, babu kuma tabbatacciyar magana”, in ji Abdulrashid.
Malam Ya’u Zawaciki, daya daga cikin sabbin Malamai da aka gaza biyan su hakkinsu, ya ce sun rubuta takarda domin ganin gwamnan don ya san halin da suke ciki amma abin ya gagari Kundila. Haka zalika, sun yi kokarin ganin Sakataren gwamnati Abdullahi Bichi amma bai samu sukunin saurara su ba.
Read also: EFCC Ta Kori Ma’aikata Sama da 40, Ta Gurfanar da Biyar Kan Cin Hanci da Rashawa
Ma’aikatan sun koka tare da bayyana rashin jin dadinsu da yadda suka tsinci kansu baya ga yadda rayuwa ta yi tsada ga kuma tarin bukatu.
A saboda haka suke rokon gwamna Abba Kabir Yusuf da ya duba halin da suke ciki ya biya su albashinsu ko sa fita daga kuncin da suke ciki.



























