Daga Abdu Ado
Read also: Rashin Kulawa Na Daga Cikin Bukatun Da Matar Gwamna Abba Ta Kai Kara A Kotu Don A Raba Su
ECOWAS ta ce idan sojojin Nijar suka gaza bin ka’idojin da shugabannin kasashen uku da ke kwamitin suka ba su, ba za a cire wa kasar takunkumai ba kuma za a duba yiwuwar amfani da karfin soji.
Kungiyar raya tattalin arzikin kasashen Yammacin Afirka (ECOWAS) ta nada kwamiti na shugabanni uku da zai tattauna da sojojin da suka yi juyin mulki a Nijar kan mayar da mulki hannun farar-hula sannan ya duba yiwuwar janye takunkuman da aka kakaba wa kasar.
Shugabannin kungiyar ta ECOWAS sun bayyana haka ne a sanarwar da suka fitar bayan taronsu na shekara-shekara a Abuja ranar Lahadi.
ECOWAS ta nada kwamitin shugabannin kasashen Togo, Saliyo da Benin domin tattaunawa da sojojin Nijar don su amince “da jadawalin mika mulki a dan kankanen lokaci” sannan su “gaggauta dawo da tsarin mulki”.
Read also: “Babu Wani Dalilin da Zai Sa Na Yi APC”, Wanna Wasan Fulani Ne da Kanuri – Sule Lamido
Shugaban Saliyo Julius Maada Bio, da shugaban Benin Patrice Talon da kuma shugaban kasar Togo Faure Gnassingbe za su gana da sojojin na Nijar domin ganin “sun bar mulki a kankanen lokaci”, a cewar kungiyar.
Labari mai alaka: Ba za mu bar Sahel Alliance ta karkatar da hankalinmu ba: Tinubu
ECOWAS ta ce: “Za a rika janye tankunkuman da aka sanya wa Nijar ne daki-daki bisa la’akari da sakamakon tattaunawar da kwamitin shugabannin kasashen ya yi da sojojin na Nijar”.
ECOWAS ta ce idan sojojin Nijar suka gaza bin ka’idojin da shugabannin kasashen uku da ke kwamitin suka ba su, ba za a cire wa kasar takunkumai ba kuma za a duba yiwuwar amfani da karfin soji.
Kazalika kungiyar ta jaddada kiran da ta yi wa sojojin Nijar na sakin Mohamed Bazoum da dukkan mutanen da suka kama ba tare da wani sharadi ba.
Read also: Mutane 16 Gini Ya Faɗawa A Unguwar Dandishe A Kano
Tun da farko, shugaban Nijeriya Bola Tinubu, wanda kuma shi ne shugaban ECOWAS, ya ce kungiyarsu za ta yi kokarin tattaunawa da kasashen da ke karkashin mulkin soji domin mayar da mulki hannun farar-hula “a lokaci kankane”.
TRT AFRICA
Domin samun labarai masu kayatarwa ka bi mu a Facebook da WhatsApp@Thestentornews.com



























