Connect with us

Hi, what are you looking for?

RA'AYI

Wacce Matatar Man Fetur Ce a Fatakwal za ta Fara aiki a Watan Disamba: Tsohuwar ko Sabuwar ko Kuma Duka?

Usman
Usman
Daga Usman Bello
Kwanan nan Gwamnatin Tarayya ta furta cewa a watan Disamba na wannan shekara matatar man fetur da ke Jihar Fatakwal za ta fara aiki.
Jin wannan albishir ya sanya ‘yan Najeriya murna da farin ciki har kunne, duk da cewa ‘yan kasar nan mun sha jin irin wannan alkawarin daga shugabanni kuma ka ji abin shiru, an aiki bawa garinsu.
Duk da cewa masu magana suna cewa sau daya maciji ke saran mutum a rami guda, shi ya sa ‘yan Najeriya suka yanke kyakkyawan zato ga alkawuran shugabanni.
Kyakkyawan misali a nan kurkusa shi ne yadda aka yaudari ‘yan kasa game da kaddamar da jirgi mai suna “Air Nigeria”  da kuma jinkirin fara samar da tataccen mai daga matatar mai ta Dangote. Wadannan da makamantan su ba za su gushe a zukatan ‘yan Najeriya da al’ummar duniya baki daya ba.
Ba abin mamaki ba ne a gyara matatar man fetur ta Fatakwal a bisa wa’adin da aka ambata, wato nan da karshen shekarar nan. To amma abin tambayar wacce matatar za a gyara; Tsohuwar ko Sabuwar ko kuma duka biyun?

Ni a sanina, matatar man Fatakwal ta kunshi rukuni guda biyu, akwai tsohuwar matata mai fitar da adadin ganga dubu 60 a rana, da kuma sabuwar matata mai fitar da ganga dubu 150 a rana. ‘Yan kasa za su so jin wacce matatar za a gyara daga cikinsu.

oil

Wannan tambayar ta faru ne sakamakon rahotanni da kafofin yada labarai suka fada sakamakon jawabin da Manajan Darakta na (NNPCL) ya furta duk da bai fayyace cikakken bayanin adadin gangar man da ake samarwa ba, a zantawarsa da manema labarai.
Yana da matukar muhimmanci ga kamfanin samar da man fetur na kasa (NNPCL) ya fayyace matatar man da za a yi wa gyaran, ko dai tsohuwar mai samar da ganga dubu 60 ko kuma sabuwar mai dubu 150 a kullum ko kuma duka, kamar yadda muka tambaya a tun da farko.
Ba sabon abu ba ne ga kamfanin NNPC ya boye ko ya ki bayar da cikakken bayanai ga al’umma game da yadda ake fitar da gurbataccen mai da kuma wanda ake amfani da shi a cikin gida. Har kullum, banbancin da ake samarwa na rarraba albarkatun man fetur a tsakankanin kamfanoni mai da hukumomin suna dawo da tataccen man fetur ciki gida Nigeriya na haifar da shakku a zukatan ‘yan Najeriya.
A kullum bayyana adadin man da ake samarwa a cikin gida yana kara haifar da shakku. Misali a watan Mayu, an ce an samar da akalla lita miliyan 69.54, haka kuma a watan Yuni aka ce ya fado zuwa lita miliyan 49.48 wato ya ragu da kaso 28.3 daga cikin 100, ya kuma sake fadowa a watan Yuli da lita miliyan 45.74, wato kaso 28.3 daga cikin 100.
Wannan rashin tabbas na alkaluma su ake sanarwa al’ummar Nigeriya a ko da yaushe.
Usman Bello kwararen Jami’in Hulda da Jama’a ne, za a iya samun sa ta adireshin ubameen.ub@gmail.com
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Advertisement

Trending

You May Also Like

Lafiya

Daga Dr. Sunusi U. Na’ibi Yadda mutum ke wanke baki da kuma irin burushin da yake amfani da shi suna iya canza lafiyar baki...

Noma da Kiwo

DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA (2) Daga Yazid Sunusi YahayaRead also: DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA UKU (3)...

Noma da Kiwo

Dabarun kiwan kaji a lokacin yanayi na sanyi Daga Yazid Sunusi YahayaRead also: DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA UKU (3) Sau...

Kano

Gwamnatin Kano Ta ƘirƘiri Sabon Tsarin Biyan Fansho da Giratuti Ta Intanet Gwamnatin Jihar Kano ta ƙaddamar da wani sabon tsari na musamman na...