Hukumar Hisbah a jihar Kano, ta ce ta fara samun kyawawan sakamako tun daga lokacin da ta yi bikin “Auren Gata” na maza da mata 1,800 a daukacin kananan hukumomin 44, na jihar a makonnin da suka gabata.
Babban Kwamandan Hukumar ta Hisbah, Malam Aminu Ibrahim Daurawa ya furta hakan ne ta hannun Mukaddashinsa kuma Babban Daraktan Hukumar (DG), Alhaji Abba Sa’id Sufi a lokacin da ya karbi bakuncin shugabannin kungiyar sa kai mai suna, “Al-Ihsan Charity Foundation” da ke Jihar Bauchi, wadanda su ka kai ziyara shalkwatan hukumar Hisbah a unguwar Sharada da ke jihar Kano.
Read also: Auren Gata Da Gwamnatin Kano Ta Yi Haramun Ne, Inji Sheik Hadi MaiHula
Alhaji Abba Sa’id Sufi ya kara da cewa, ga dukkan alamu shirin Auren Gata na hukumar Hisbah laya ta yi kyan rufi, domin ya fara yaduwa izuwa makwabtan jihohi, kuma ya zaburar da shugabannin kungiyoyin sa kai da walwalar jama’a don daukar nauyin shirin Auren Gata, a tsakanin marayu, da marasa karfi da ke cikin al’umarsu.
Shugaban ya ce wanna ba karamin ci gaba aka samu ba, baya ga sake samun daukaka da daraja a idanun jama’ar jihar Kano da fadin tarayyar Najeriya da ma makwabtan kasar nan.
Read also: “Na Fasa Auren Yar Guda”, In ji Mai Wushirya
Babban Daraktan ya sake yin kira ga sauran kungiyoyin jin kan marasa karfi da su dukufa domin samun sahihan mafita da magance matsalar yada ayyukan barna a tsakanin matasa da sauran jama’a.
Alhaji Abba Sa’id Sufi ya yi alkawarin ba wa kungiyar sa kai ta “Al-Ihsan Charity Foundation” Bauchi, hadin kai da goyon baya don samun nasara ga shirin da suka sa a gaba na auren ‘yan mata, marayu da marasa karfi ya samu gagarumar nasara.
Tun da fari a jawabinsa, Shugaban kungiyar sa kai ta “Al-Ihsan Charity Foundation”, Bauchi, Alhaji Abubakar S. Bayero ya ce, shi da tawagar mambobin kungiyar sun kawo ziyara ne ga hukumar Hisbah ta jihar Kano, duba da yadda jami’an hukumar suka yi fice a harkokin Auren Gata, kuma hukuma ce tamkar da dubu a Najeriya.
Read also: EFCC Ta Kori Ma’aikata Sama da 40, Ta Gurfanar da Biyar Kan Cin Hanci da Rashawa
Alhaji Abubakar S Bayero, ya ce kungiyarsa ta “Al-Ihsan Charity Foundation” ta shirya tsaf don yin bikin auren marayu da ‘ya’yan marasa karfi mutum 100 a jihar Bauchi, ya kuma ce makasudin zuwa hukumar Hisbah shi ne su fadada ilimi akan harkokin Auren Gata wanda hukumar ta yi bikinsa a kwanakin baya a bisa jagorancin Gwamna Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf.
Jami’in Hulda da Jama’a da manema labarai na Hukumar Hisbah ta Kano, Malam Lawan Ibrahim Fagge ya aiko mana cewa shugaban kungiyar ya mika godiyarsu ta musamman ga mukaddashin Babban Kwamandan hukumar Hisbah, Alhaji Abba Sa’id Sufi,( DG HISBAH) bisa yadda ya tarbe su, baya ga ba su shawarwari masu nagarta da suke da ruwa da jibi game da harkokin “Auren Gata” domin samun makama mai kyau.



























