Kotun ɗa’ar ma’aikata ta dakatar da gamayyar kungiyoyin ƙwadago na NLC da TUC daga shiga yajin aikin da suka daura a niyyar yi a ranar Talata 14 ga watan Nuwamba.
Alƙalin kotun, mai shari’a Benedict Kanyip ne ya yanke hukuncin dakatar da yajin aikin bayan ƙarar da gwamnatin Najeriya da ministan shari’ar ƙasar suka shigar gaban kotun suna neman kotun ta hana ƙungiyoyin shiga yajin aikin, saboda hakan zai iya jefa ‘yan ƙasar cikin ƙarin wahala.
Lauyan masu gabatar da ƙarar Barista Tijani Gazali ya ce matsawar ba a dakatar da ƙungiyoyin daga shiga yajin aikin ba, za a iya samun tayar da hargitsi tare da kawu ruɗani a fadin ƙasar.
Read also: Kotun Kano Ta Yanke Wa Mutum Biyu Hukuncin Kisa Sau Bakwai Kowanne Saboda Kashe Mace Da Yara Shida
Read also: Kotu ta Umarci Masu Barkwanci Na TikTok A Kano Dasu Yi Aure Bayan Yaɗa Bidiyon “Futsara”
Read also: Kotu Ta Rufe Asusun Hisbah A kano, Bisa Ƙin Biyan N800,000 Ga Masu Otel
Yayin da yake hukuncin, alƙalin kotun ya ce kotun na da hurumin shiga tsakani domin hana duk wani abu da ka iya tayar da hankula a ƙasar.
Mai shari’a Kanyip ya yi amfani da sahe na 17 da 19 na kundin dokokin kotun wajen dakatar da yajin aikin.




























