Connect with us

Hi, what are you looking for?

Labarai

Shugaban Karamar Hukuma Ya Zargi Kwamishina Da yin Katsalanda Ga shugabancin Kasuwar ‘Yan Goro

Img 1697218038671

Shugaban Karamar Hukumar Kumbotso ta Jihar Kano, Hassan Garba Kauye Farawa, ya yi kakkausar suka da yin Allah-wadai da yunkurin Kwamishinan Kasuwanci, Ciniki da Masana’antu na Jihar Kano Alhaji Abbas Sani Abbas na yin katsalandan da Kuma kokarin tsige Shugaban Kasuwar ‘yan Goro Alhaji Salisu Auwal (Dan Alaye) dake Mariri daga kan kujerar sa.

A wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban, Shazali Sa’ad Saleh Farawa ya aike wa manema labarai ciki har da The STENTORNEWS, ya ce Kasuwar Mariri ta zama babbar cibiyar kasuwanci a tsakanin al’ummar yankin da ma makobta, wanda ke ba da gudummawa sosai ga tattalin arzikin yankin da kuma rayuwar jama’a da dama a jihar Kano.

A cewar sa yunkurin tsige Shugaban kasuwar ya haifar da damuwa gami da rashi kwanciyar hankali da kuma makomar kasuwar.

“Ina kira ga masu ruwa da tsaki da su shiga tattaunawa mai ma’ana da kuma kokarin hadin gwiwa don magance duk wata matsala da ta shafi harkokin kasuwancin da samar da kudurin da zai tabbatar da ci gaba da wadata da kwanciyar hankali a kasuwar,” in ji shugaban.

Sanarwar ta kara da cewa shugaban Kasuwar da ake zargi yayi kaka gida a shugabancin ya himmatu wajen samar da yanayi mai kyau da cigaban harkokin kasuwanci ga ‘yan kasuwa a yankin.

“Muna kira ga gwamnatin jihar Kano, karkashin jagorancin Injiniya Abba Kabir Yusuf da ta yi la’akari da irin tasirin da irin wadannan ayyuka ke haifarwa ga tattalin arzikin yankinmu da kuma rayuwar mazauna yankin,” inji shi.

“A shirye muke domin tattaunawa da duk bangarorin da abin ya shafa don cimma matsaya mai dorewa. Hadin kai da fahimtar juna zasu taka muhimmiyar rawa da cigaban Kasuwar ta Mariri,” in ji shi.

Haka Kuma shugaban ya nuna damuwarsa tare da yin kakkausar suka ga ta’addanci da wasu da ba a san ko su waye ba, a inda wasu mutane suka jagoranci gungun ‘yan daba suka shiga ofishin shugabancin Kasuwar, tare da kwace masa kadarorinsa da muhimman takardu.

Ya ce, “Muna kira ga Alhaji Abbas Sani Abbas da ya sake duba duk wani shiri da zai kawo cikas ga zaman lafiya a Kasuwar Mariri, mun jajirce wajen tabbatar da zaman lafiya da tsaro a cikin al’ummarmu kuma za mu dauki dukkan matakan da suka dace don ganin an yi adalci ga kowa.”

Shugaban karamar hukumar ya jadadda cewa Kasuwar Yan Goro ta Mariri Mallakin karamar hukumar Kumbotso ce, ba ta ma’aikatar kasuwanci ba.

Wakilinmu ya tuntubi Kwamishina Ma’aikatar Kasuwanci da Masana’antu na Jiha, Alhaji Abbas Sani Abbas ta wayar hannu, don jin ta bakinsa game da wannan zargi, inda Kwamishina ya ce komai yana da tsari da Kuma tanadi da doka ta samar.

Alh. Abbas ya ce tuni wa’adin tsohoffin shugabanin ya Kare wanda shi ya bayar da damar aka gudanar da masalaha Kuma aka rantsar da sabbi.

“Don haka karamar hukuma bata da hanu game da kasuwa ko shugabancin ta, ya kamata jama’a kowa ya tsaya bisa hurimin da doka ta bashi”, inji Abbas

 

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You May Also Like

Lafiya

Daga Dr. Sunusi U. Na’ibi Yadda mutum ke wanke baki da kuma irin burushin da yake amfani da shi suna iya canza lafiyar baki...

Noma da Kiwo

DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA (2) Daga Yazid Sunusi YahayaRead also: DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA UKU (3)...

Noma da Kiwo

Dabarun kiwan kaji a lokacin yanayi na sanyi Daga Yazid Sunusi YahayaRead also: DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA UKU (3) Sau...

Kano

Gwamnatin Kano Ta ƘirƘiri Sabon Tsarin Biyan Fansho da Giratuti Ta Intanet Gwamnatin Jihar Kano ta ƙaddamar da wani sabon tsari na musamman na...