Daga S A Ƙ/Na’isa
Shugaban rikunin kamfanonin Ɗangote, Alhaji Aliko Ɗangote ya nisanta kansa da wani labari da ake yaɗawa a kafafen sada zumunta na zamani cewa ya fi ‘yan Najeriya shan wahalar tsadar rayuwa, inda ya ce labarin ba shi da tushe kuma ƙirƙirare ne.
Read also: Rashin Kulawa Na Daga Cikin Bukatun Da Matar Gwamna Abba Ta Kai Kara A Kotu Don A Raba Su
“Babu inda na ce na fi ‘yan Najeriya shan hahalar tsadar rayuwa, amma ina fatan matsalar ta zamo tarihi”, Dangote ya ce.
Ɗangote ya tabbatar wa da ‘yan ƙasa cewa, wasu ne suka ɗauki nauyin yaɗa labarin domin ɓata masa suna a dai-dai lokacin da ‘yan Najeriya ke cikin halin ƙaƙa-na-ka-yi saboda wahalhalun da ake fama da su.
Sanarwar ta nemi ‘yan kasar nan da su yi watsi da labarin, inda Ɗangote ya yi fatan kawo ƙarshen matsalar da ake ciki a Najeriya. “Duk abin da ya shafi ‘yan Najeriya ya shafe mu”, in ji Sanarwar.
Read also: Ingila Za Ta Haramta wa Dalibai Amfani da Wayoyin Hannu a Makarantu
Ɗangote ya ƙara da cewa, ”An kawo maganar faɗuwar darajar Naira da sayen kaya da Dalar Amurka ne domin cimma wasu buƙatu na ƙashin kai buƙatun da ba su samu damar biya ba a baya.”
Kamfanin na Ɗangote na sarrafa siminti da takin zamani da kuma matatar man fetur. A ɓangaren kayan abinci kuma, kamfanin na sarrafa sikari, gishiri da kayan dandanon girki ne kaɗai.
“Mu ma muna sayen muhimman kayan abinci a kasuwa kamar yadda kowa ke saya don amfanin kanmu da kuma bayarwa wajen ciyar da al’umma.” In ji Ɗangote.
Shugaban kamfanin ya yi mamakin yadda ake neman haddasa saɓani tsakanin kamfanonin Ɗangote da ɓangaren gwamnatin tarayya, inda ya ce shi ɗan kasuwa ne ba ɗan siyasa ba, don haka babu inda ya yi maganar ƙalubalantar gwamnatin tarayya.
Read also: China Na Goyon Bayan Shugaba Tinubu, Kuma Tayi Tur Da Barazanar Trump Ga Najeriya
“Kamfaninmu ya kasance mai bin dokokin ƙasa a ko da yaushe, tare da neman sauƙi ga al’umma da fatan alheri.”
Saboda haka, sanarwar ta nemi ‘yan Najeriya da su guji ɗaukar saƙon da yake ba daga kamfanin yake kai tsaye ba, tare da yaɗa raɗe-raɗi da jita-jita wanda ba zai kawo alfanu ga kowa ba.



























