Kwamitin tallafawa ilimi na ƙaramar hukumar Maƙarfi a kwanan nan ya karrama biyu daga cikin ‘yan asalin yankin, Farfesa Aisha Abdulƙadir da Farfesa Gausu Ahmad, saboda nasarorin da suka samu na ilimi da kuma gudunmawar da suka bayar a fannonin su daban-dabam.
Farfesa Abdulƙadir, Shugaban Sashen Kimiyyar Ƙasa da ke Cibiyar Binciken Aikin Gona (IAR) a Jami’ar Ahmadu Bello Zariya, da Farfesa Ahmad, na Sashen Nazarin Koyar da aikin Jarida da ke Jami’ar Bayero Kano, an bawa kowannensu lambar yabo ta ƙwarewa a lokacin bukukuwa daban-dabam da aka gudanar a jami’o’insu.
Taron bayar da kyautar, wanda aka gudanar daban-dabam a jami’o’in biyu, ya samu jagorancin, Hakimin ƙaramar hukumar Makarfi, Alhaji Adamu Abdullahi, a inda ya yaba wa farfesoshin a matsayin abin koyi da kuma gamsuwa da gudummawar da suka bayar ga makarantu da kuma ci gaban al’ummar yankin da ƙasa baki ɗaya.
Alhaji Abdullahi ya jinjina wa Farfesa Abdulkadir bisa jajircewarta na ciyar da martabar noma gaba da ɗinke ɓarakar da ke tsakanin masana ilimi da kuma manoma sannan ya bayyana Farfesa Ahmad a matsayin jami’in ilimi wanda ya raya matasa da suka rungumi aikin jarida a matsayin sana’a.
Read also: An Yi Kira ga Karamar Hukumar Sumaila da ta Samar da Bandaki a Makarantar Liman Yau JASS Sumaila
Alhaji Mahmud Gazara, Shugaban kwamitin Ilimi, a ƙarƙashin ƙungiyar , ya ce yana daga al’adar ƙungiyar na karrama mutane da suka cimma wani matsayi mai daraja a rayuwa irin wannan. Ya bayyana fatan cewa nasarorin da suka samu za su ƙarfafi gwiwar matas a yankin domin su yi koyi.
Taron karramawar ya samu halartar manyan baƙi daga jami’o’i biyu da kuma al’ummar Maƙarfi da Hakimin Ƙaramar hukumar da mambobin Kwamitin da ke jagorantar shirn.
Read also: Ingila Za Ta Haramta wa Dalibai Amfani da Wayoyin Hannu a Makarantu
A Jami’ar Ahmadu Bello, wakilai daga IAR sun haɗar da Farfesa. Ado A. Yusuf (Babban Darakta), Farfesa. S. B. Abdu (Dean, Faculty of Agriculture), Farfesa. Nafiu Abdu (Mataimakin Darakta), da Dakta. Sharhabil M. Yahaya (Shugaban, Ayyukan Fadada Noma). Al’ummar ƙaramar hukumar Maƙarfi sun samu wakilcin Alhaji Adamu Abdullahi (Hakimin Maƙarfi), Alh. Bako Mamuda (Shugaban Kwamiti), Alhaji Kabiru Abdullahi Sada (Dagacin Maƙarfi), Hon. Samaila Aliyu, Farfesa. Lawal Saidu, da Nuhu Suleiman Maƙarfi.
A Jami’ar Bayero Kano, an yi bikin ne da haɗartar Farfesa. Umar Pate (Vice Chancellor, Federal University Kashere Gombe State), Prof. Abdallah Uba Adamu (Tsohon Mataimakin Shugaban Jami’a, National Open University of Nigeria), Farfesa. Umar Faruk Jibril (Dean, Faculty of Communication), Farfesa. Ahmad Muhammad Maƙarfi (Tsohon Jakadan Najeriya a Brazil), Farfesa. Mainasara Shugan Sashin Koyar da Aikin Jarida (Head, Mass Communication Department), da Dr. Musa Labaran.



























