Daga Wakilinmu
Gwamnatin jihar Kano ta yi bayani ƙarara kan tanade-tanaden dokar aure da ta ya mutsa hazo har ta janyo muhawara a jihar Kano a kafaffen yaɗa labarai da sauran shafukan sada zumunta.
Read also: Wasu Ma’aikatun Gwamnati Zasu Sami Sabbin Shugabanni A Kano
A hirar sa da kafar yaɗa labarai ta BBC, Kwamishinan shari’a na jihar Barista Haruna Isa Dederi ya ce tabbas akwai dokar da ta yi bayani dalla-dalla kan yadda ya kamata mutane su riƙa gudanar da auratayyar su a jihar.
“Doka ce da aka ƙirƙire ta tun 1988, kuma a sashi na biyar na dokar wannan bayani yake.Inji Dederi.
BaristaHaruna Dederi ya ce dokar ta yi bayani kan mene ne ya halasta da kuma mene ne aka haramta idan an tashi yin aure a jihar Kano.
“Ba iya lefe kawai dokar ta haramta ba, amma a yanzu shi ne abin da ya fi ɗaukar hankalin al’umma,” in ji kwamishinan.
“Lokaci zuwa lokaci akan sake bibiyar doka, domin sake mata fasali idan buƙatar hakan ta taso.
“Tsayin zamani da kuma buƙatuwar mutane kan sa na sauya doka, ko kuma a yi mata kwaskwarima. Kamar dai yadda ake yi wa kundin tsarin mulki na ƙasa,” in ji Barr. Dederi.
Read also: Gwamnatin Kano Ta Rufe Film House Da Ke Unguwar Dorayi, Mutane na Sambarka
Kwamishinan ya tabbatar cewa a iya saninsa babu wanda ya gabatar da bibiyar wannan doka domin sabunta ta, ko kuma sauya mata fasali.
A cewarsa matuƙar akwai doka, duk tsayin zamani idan ba a yi mata gyara ba tana nan a matsayin doka babu mai sauya hukuncinta.
An tambayi Dederi kan me yasa dokar ta ɗauki kusan shekara 36 amma da dama a cikin al’umma ba su santa ba?
Ya ce ƙalubale ne masu yawa da suke janyo haka, inda ya fara da zayyana yawan dokokin da ake da su a tarayya da jihohi. ya kuma ba da shawarar kamata ya yi a haɗa kundin wuri guda domin taƙaita yawan dokokin.
Ƙalubale na biyu shi ne ɓangaren shari’a na buƙatar a riƙa wayar da kan al’umma kan irin waɗannan dokoki. Saboda da ƙuduri baya zama doka sai ya bi matakai da dama, tun a lokacin matakan ya kamata a riƙa sanar da al’umma a kanta.
Kazalika idan majalisar dokoki ta jiha ta tabbatar da doka ya kamata a riƙa samar da sashe da zai riƙa shaidawa mutane dokar.
Masu aiwatar da dokar ma ya kamata su riƙa ilimantar da mutane game da dokokin da ake yi musu hukunci a kai, ba sai ranar da hukunci ya zo ba mutum ya ji ta, a matsayin sabuwar doka a kansa.
Kwamishinna Haruna Isa Dederi ya amsa cewa akwai ƙarancin wayar da kan al’umma game da dokokin rayuwa da suka shafe su, wanda kuma haka aikin gwamnati ne tai nazari da fito da dabaru na ilimantar da al’umma.




























