Daga Wakilinmu
A ranar Litinin akai jana’izar wani magidanci da matarsa da ‘ya’yansa biyar da suka rasu sanadiyar tashin gobara a gidan sa da ke titin Ahmadu Jibril Maigoro a unguwar Tudun Wada Bompai a Karamar hukumar Nasarawa a cikin garin Kano.
Read also: Gobara : Kasuwar Ƴan Katako A Kano Ta Kama da Wuta
Mai unguwar Tudunwada, Ahmad Tijjani Yau, yana daga cikin shaidun gani da ido ya ce, gobara ta tashi da misalin karfe 12:30 na daren ranar Lahadi.
Mai unguwar, ya fadi cewa sanadiyar tarratsin wutar lantarkin ne ya haifar da gobarar hakan yai sanadiyar kamawar wutar kuma ta kai ga na’urar sanyaya lemo wato furinji yai bindiga wanda wutar ta warwatsu a gidan.
Read also: Gobara Ta Kone Gidaje, Na’urar Wutar Lantarki a Kano
Alhaji Tijjani Yau, a zantawarsa da manema labarai ya tabbatar da hayaki ne yayi sanadiyar rasuwarsu gaba daya baya ga kokarin makota na bude kofar gidan amma hakan ta gaggara, daga bisani, da kokarin tallafin hukumar kashe gobara ta jiha aka bude, amma aka tarar sun galabaita.
Wadanda suka rasun sun hadar da mai gidan Malam Shu’aibu Ahmad mai kimanin Shekaru 56 da matarsa Binta Shu’aibu me shakara 37. ‘ya’yen sun hadar da Zainab mai shekara 15 da Hauwau 13 da Ummukulsum shekara 10 da Hanifa mai shekara 7 da Aisha ‘yar shekara 4 da Kuma Ahmad mai shekara 2.
Read also: Gobara ta ƙone Gidan Tsohon Gwamnan a Abuja ƙurmus
Ya ce bayyan kai su asbitin Abdullahi Wase dake cikin garin Kano, likita ya tabbatar da rasuwar su. Kuma tuni akai jana’izarsu kamar yadda addinin musilinci ya tanadar.



























