Daga Abdu Ado
Read also: Wasu Ma’aikatun Gwamnati Zasu Sami Sabbin Shugabanni A Kano
Umahi ya ce ma’aikatar ta kafa kwamitoci shida saboda yankunan siyasa shida na kasar nan domin tantance basukan da ‘yan kwangila ke bin ta.
Ya ce, kwamitocin za su tantance takardun shaidar bashin da gwamnati ta ba wa ’ya kwangilar zuwa ranar da Buhari ya sauka daga mulki.
Read also: Ban taɓa cin haram ba a shekaru 35 a aikin Gwamnati a Najeriya, in ji Barista Mainasara Kogo
Za kuma su tantance takardun shaidar bashin da suke bin ma’aikatar daga hawan Shugaba Tinubu zuwa yanzu.
Umahi ya ce tantance basukan da kuma sauyin farashi da aka samu na da muhimmanci, lura da hauhawan farashin kaya.
Read also: Bashi Ko Ceton Rai? Kukan zuci da Siraɗin da Ma’aikatan Gwamnati ke ciki a Nigeria
Don haka ya shawarci ’yan kwangilar da su zo gaban kwamitin domin tantancewa a hedikwatar ma’aikatar da ke Abuja.
Sakataren yada labaran ma’aiaktar, Orji Uchenna Orji ya ce, za ya yi tantancewar ne daga ranar Talata 12 zuwa Juma’a 22 ga watan nan na Disamba daga karfe 9 na safe zuwa 7 na dare.




























