Shalkwatar tsaron Najeriya ta bayyana harin jirgi maras matuƙi na baya-bayan nan da aka kai Tudun Biri a jihar Kaduna wanda ya halaka mutum kusan 100 a matsayin abin tashin hankali da ba a buƙatar ya sake faruwa a nan gaba.
A sanarwar da Daraktan yaɗa labarai, Manjo Janar Edward Buba ya fitar, an kai harin ne sakamakon bayanan sirrin da aka samu cewa akwai ƴan bindiga a yankin.
Read also: ‘Yan Bindiga Sun Kai Hari Asibitin Kaduna Tare da Sace Ma’aikatan Jinya
Harin dai ya faru ne dai-dai lokacin da mutane a ƙauyen Tudun Biri suke gudanar da taron bikin Mauludi.
Read also: Ingila Za Ta Haramta wa Dalibai Amfani da Wayoyin Hannu a Makarantu
Tuni dai gwamnan jihar ta Kaduna, Uba Sani ya ba da umarnin gudanar da bincike mai zurfi kan lamarin da ya jikkata wasu gommai.
Rundunar sojin ƙasar ta ce lokaci zuwa lokaci ta kan ƙaddamar da irin wannan hari kan ƴan bindiga da a wani lokacin yake shafar al’ummar gari.
Read also: Jita-Jitar Juyin Mulki Ba Gaskiya Bane Kuma Makirci Ne — Shelkwatar Tsaro
Zuwa yanzu, waɗanda suka jikkata suna samun kulawa a asibitin gwamnati a jihar.
Jihar Kaduna na fama da matsalar tsaro inda tsawon shekaru, ƴan bindiga ke kai hare-hare tare da yin garkuwa da jama’a don neman kuɗin fansa.(BBC)




























