Fitattacen Malamin Addinin Musulunci na Jihar Kano, Sheikh Yusuf Ali (Sarkin Malaman Gaya), ya koma ga Allah yana da shekaru 73 a daren jiya Lahadi.
Sanarwar rasuwar mashahurin Malamin ta fito ta hannun dansa Muslihu Yusuf Ali ta kafar sadarwasa ta Facebook a daren Lahadin.
Read also: Tsohon ma’aikacin gidan rediyo Kano, Malam Ali Sufi Utai, ya rasu
An haifi Sheikh Yusuf Ali a shekarar 1950, a garin Gaya da ke Jihar Kano. Bayan karatuttukan da ya yi a fannin addini da Sharia, ya zama ma’aikacin kotun Shariar Musulunci a shekarar 1974, a inda ya kai matsayin Rajistara a babbar kotun Shariar Musulunci. Ya kuma zama darakta a wannan kotun.
Read also: Gwamnatin Kano Ta Naɗa Sheikh Bazzallah Nasir Kabara A Matsayin Shugaban Hukumar Tace Fina-finai
Sheikh Yusuf Ali ya yi ritaya daga aiki a shekarar 2009. Ya kuma ci gaba da koyarwa da yada da’awa da kuma samar da magunguna ga marasa lafiya musamman masu shafar aljannu.
Read also: One Kano Agenda: Gwamna Yusuf Ya Nuna Samun Haɗin Kai Shine Mabuɗin Farfaɗo da Jihar Kano
Za a yi jana’izarsa a yau Litinin a Masallacin Murtala da ke unguwar Hausawa da ke kan titin zuwa gidan namun daji da karfe 1:30 na rana.
Allah Ya ji kansa da rahama.




























