Connect with us

Hi, what are you looking for?

Labarai

Gwamna Kano ya Amince a Biya Masu Aikin Shara Albashinsu Naira Miliyan 39

SN

Gwamnatin jihar Kano ta amince da fitar da kudi kimanin Naira miliyan 39 domin biyan bashin da ma’aikatan wucin-gadi na Hukumar Kwashe Shara ta jihar suke bi na kimanin watanni biyar.

Shugaban hukumar kwashe sharar ta jihar Kano Ambasada Ahmadu Haruna Zago ne ya bayyana hakan a wani taron manema labarai da ya kira.

Idan za a iya tunawa, Hukumar Karbar Korafe-Korafe ta tarayya da ke Kano da ma Hukumar Hukuntawa da Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta Kasa ICPC sun sha alwashin tattaunawa da gwamnatin Jihar Kano domin ganin an biya masu kwasar sharar alawus-alawus dinsu na watanni 16 da suke bi.

Danzago ya ce biyo bayan tantancewa da kwamitin kar-ta- kwana da hukumar ta kafa ya tantance tare da mika rahotonsa, kuma gwamnan Kano Abba Kabir Yusif ya amince da biyan kudin cikin gaggawa domin inganta ayyukan tsafta a jihar Kano.

Ahmadu Zago ya ce kowane lokaci daga yanzu ma’aikatan wucin gadin za su fara karbar kudinsu ta hanyar banki ya kuma horansu da su domin su kasance masu kula da ayyukansu a ko da yaushe a dukkanin sako da lungu na jihar nan.

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You May Also Like

Lafiya

Daga Dr. Sunusi U. Na’ibi Yadda mutum ke wanke baki da kuma irin burushin da yake amfani da shi suna iya canza lafiyar baki...

Noma da Kiwo

DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA (2) Daga Yazid Sunusi YahayaRead also: DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA UKU (3)...

Noma da Kiwo

Dabarun kiwan kaji a lokacin yanayi na sanyi Daga Yazid Sunusi YahayaRead also: DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA UKU (3) Sau...

Kano

Gwamnatin Kano Ta ƘirƘiri Sabon Tsarin Biyan Fansho da Giratuti Ta Intanet Gwamnatin Jihar Kano ta ƙaddamar da wani sabon tsari na musamman na...