Kwamiti Ya Kama Jabiru Sanda Zage da Kwalaben Kodin 151 a Kano, Ya Fuskanci Hukunci Kotu
Daga Wakilin mu
Kwamitin kar-ta-kwana na yaƙi da ta’ammali da miyagun ƙwayoyi da daba a Kano, ƙarƙashin jagorancin Muhyi Magaji Rimin Gado Esq., ya kama Jabiru Umar Sanda Zage da kwalaben kodin 151 a ɗakinsa, tare da gurfanar da shi a gaban kotu.
Read also: Kotun Kano Ta Yanke Wa Mutum Biyu Hukuncin Kisa Sau Bakwai Kowanne Saboda Kashe Mace Da Yara Shida
Kotun Mai Lamba 44 da ke Gwammaja, Kano, ƙarƙashin Mai Shari’a Muhammad Alhaji Isa, ta yanke masa hukuncin ɗaurin shekara ɗaya kan mallakar kayan maye, da kuma wata shekara ɗaya kan laifin ajiye mata a ɗakinsa.
Kotun Tarayya a Gombe Ta Soke Zaben da Aka Yiwa Farfesa Isa Ali Pantami
Read also: Kotu Ta Daure Wani Mutum Wata 3 A Gidan Gyaran Hali Sakamakon Kona Taya A Kano
Lauyan da ya gabatar da shi a gaban kotun, Auwal Abdulkadir Sani Esq., ya ce an kama Zage da kwalaben kodin 151 tare da mata uku da ake zargin suna cikin maye.
An gurfanar da shi kan zargin shiga ƙungiyar masu aikata laifuka, ta’ammali da kayan maye, ba da mafaka ga mata da masu aikata laifuka, da kuma damun jama’a.
Sai dai kotun ta same shi da laifi kan mallakar kayan maye da kuma ajiye mata a ɗakinsa, inda ta yanke masa hukuncin ɗaurin shekara ɗaya kan kowane laifi.
Read also: Kotun Ƙoli Ta Kammala Sauraron Ƙarar Zaɓen Kano, Za Ta Sanar Da Ranar Yanke Hukunci
“Ku Bar Ofisoshi Ko Ku Fuskanci Hukunci,” Gwamnatin Kano Ta Gargadi Ma’aikatan Da Suka Kai Ritaya
Bayanan da aka samu ba su fayyace ko za a yi zaman hukuncin biyu ne a lokaci guda ko kuma ɗaya bayan ɗaya ba





























Pingback: Wasu Ma'aikatun Gwamnati Zasu Sami Sabbin Shugabanni A Kano - The StentorNews Hausa