Connect with us

Hi, what are you looking for?

Tsaro

Sarkin Noma Nadabo Chiromawa Ya Kubuta, Yana tare da Iyalan Sa

Sarkin Noma Kano, Alh Yusuf Nadabo
Sarkin Noma Kano, Alh Yusuf Nadabo

Sarkin Noma Nadabo Chiromawa Ya Kubuta, Yana tare da Iyalan Sa

Daga Wakili mu

A halin yanzu hankali ya fara kwanciya a Karamar Hukumar Garun Mallam bayan da wasu rahotanni suke tabbatar da an samu sahihan bayanai na kuɓutar Sakin Noma Alh Yusuf Nadabo dake garin Chiromawa.

Wata majiya ta sheda mana cewa Sarkin Noma Alhaji Nadabo Chiromawa, ana zargin ya kubuta daga hannun masu garkuwa da mutane bayan da suka yi awon gaba da shi a daren jiya Assbar, kuma a halin yanzu yana gida tare da iyalinsa cikin koshin lafiya.

Rahoton Kwararu Ya Ce Hare-Haren Garkuwa Da Mutane Ya Ƙaru da Kaso 66% Akan Shekarar 2025 A Najeriya

Majiya ta ce yunƙurin da al’umma gari da jami’an tsaro suka yi ya taimaka wajen hana maharan su sami sukunin tafiya da shi nesa, kuma suka sake shi.

Amma ya zuwa haɗa wannan rahoton TSN Hausa bata samu cikakken bayani daga jami’an tsaro na yadda ya kubuta ba.

Gwamnatin Kano Ta Sanar da Hutun Bikin Takutaha
A daren jiya Asabar ne wasu ƴan bindiga sukai tsinke a garin Chiromawa dake Karamar Hukumar Garun Mallam inda suka kashe mutane uku suka kuma jikata mutane biyar tare da garkuwa da Alhaji Yusuf Nadabo.

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You May Also Like

Lafiya

Daga Dr. Sunusi U. Na’ibi Yadda mutum ke wanke baki da kuma irin burushin da yake amfani da shi suna iya canza lafiyar baki...

Noma da Kiwo

DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA (2) Daga Yazid Sunusi YahayaRead also: DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA UKU (3)...

Noma da Kiwo

Dabarun kiwan kaji a lokacin yanayi na sanyi Daga Yazid Sunusi YahayaRead also: DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA UKU (3) Sau...

Kano

Gwamnatin Kano Ta ƘirƘiri Sabon Tsarin Biyan Fansho da Giratuti Ta Intanet Gwamnatin Jihar Kano ta ƙaddamar da wani sabon tsari na musamman na...