Connect with us

Hi, what are you looking for?

Ilimi

Auren Gata Da Gwamnatin Kano Ta Yi Haramun Ne, Inji Sheik Hadi MaiHula

Sheik Hadi MaiHula
Sheik Hadi MaiHula

Auren Gata Da Gwamnatin Kano Ta Yi Haramun Ne, Inji Sheik Hadi MaiHula

Daga Wakilinmu

Wani Shehin Malamin Addinin Musulunci a jihar Kano Sheik Alaramma Hadi Inuwa Maihula Sanka ya ce Auren zawarawa ko gata da gwamnatin Jihar Kano ta yi Haramun ne domin Allah maɗaukakin Sarki bai ɗorawa bawansa dole yayi Aure ba, sai wanda yake da iko.

Sheik Hadi MaiHula ya bayyana hakan ne a tattaunawarsa da ‘yan Jaridu a Kano da yammacin talatar nan.

Ya ce Al’qur’ani mai girma yayi bayanin cewa fitar da Zakka da zuwa aikin Hajji da kuma yin Aure sai wanda yake da ikon yi, yana mai cewa aure Addini ne, amma dibban kuɗin talakawa da gwamnatocin jihohi ke kashewa domin yin auren zawarawa ko auren gata “Haramun ne.” Ana kashe kuɗaɗen al’umma a hanyoyin da basu da ce ba, yayin da mutanen Kano suka rasa ingantaccen ruwan sha da wadatattun asibitoci da makamantansu.

Rashin Bin Ƙa’idar Gini, Gwamnatin Kano Ta Rusa Dogon Bene A Nassarawa GRA

“Da Aure da Zakka da zuwa aikin Hajji ba’a taɓa ɗorawa wani ya zama dole ba matukar bashi da iko,” inji Malamin.
Malamin ya kafa hujja da cewa “Allah yayi bayani a cikin Suratul Nur da Hadisan Imam Muslim da Bukhari suka rawaito,” inji MaiHula.
Malamin ya ce wasu daga cikin shugabannin da suka yi a baya ma sunyi nadamar aikata hakan, yana mai Jan hankalin gwamnatin Jihar Kano ta da dakatar da aikata hakan a nan gaba.

“Garin Kano ya fi buƙatar wadatattun asibitoci da wadatattun kwararrun likitoci da ruwan sha da biyan mutanen da suka yiwa al’umma aiki wato ‘Yan Fasho a halin yanzu, inda ya ce ba by hujja a kwashi makudan kuɗaɗen al’umma ayi abun da bai da ce ba,” inji MaiHula.

“Tun daga Gwarzo ko Takai ko Tsanyawa al’umma suke tahowa asibitin kwararrun na Murtala, kuma asibitin nan tun 1928 aka yi shi, me yasa baza a gina irin asibitin a Takai ko Tsanyawa ko Gwarzo ba ?” Inji Alaramma.

Fursunoni 61 Sun Haddace Alƙur’ani Mai Tsarki a Gidan Gyaran Hali na Kano

Daga ƙarshe ya yi fatan gwamnatin Jihar Kano da sauran jihohi da suke da tunanin Ire-iren wannan aure zasu dena, yana mai cewa Idan akayi auren, gwamnatin ita zata ciyar musu da Matar ne ko kuma zata ɗauki nauyin biya musu kuɗin hakika idan matan sun haihu, ya ƙara da cewa maimakon haka kamata yayi gwamnatin Jihar Kano ta koya musu sana’o’in dogaro da kai maimakon ɓarnatar da dukiyara al’umma a hanyar da bata da ce ba, da sunan auren gata.

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You May Also Like

Lafiya

Daga Dr. Sunusi U. Na’ibi Yadda mutum ke wanke baki da kuma irin burushin da yake amfani da shi suna iya canza lafiyar baki...

Noma da Kiwo

DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA (2) Daga Yazid Sunusi YahayaRead also: DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA UKU (3)...

Noma da Kiwo

Dabarun kiwan kaji a lokacin yanayi na sanyi Daga Yazid Sunusi YahayaRead also: DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA UKU (3) Sau...

Kano

Gwamnatin Kano Ta ƘirƘiri Sabon Tsarin Biyan Fansho da Giratuti Ta Intanet Gwamnatin Jihar Kano ta ƙaddamar da wani sabon tsari na musamman na...