Connect with us

Hi, what are you looking for?

Kotu

HUKUMAR ICPC TA GURFANAR DA LIKITAN NASIRU ELRUFAI A GABAN KOTU

Nasiru El Rufa'i
Nasiru El Rufa'i

HUKUMAR ICPC TA GURFANAR DA LIKITAN NASIRU ELRUFAI A GABAN KOTU

Daga Muazu Hardawa Bauchi

Hukumar yaki da rashawa ta ƙasa ICPC ta gurfanar da kwarraren likita na Babban Asibitin ƙasa dake Abuja, Farfesa Bello Abubakar a gaban Babbar Kotun Birnin Tarayya Abujan bisa tuhumar sa da zargin rubuta sakamakon bogi game da koshin lafiyar tsohon gwamnan jihar Kaduna Malam Nasiru El-Rufa’i.
Hukumar  na zargin Farfesa Abubakar da shiryawa tare da fitar da sakamakon bogi wadda ya nuna tsohon gwamnan na Kaduna na cikin matsanancin rashin ƙoshin lafiya, inda a ranar 10 ga watan  na Yuni 2026,  lauyoyin Malam El-Rufa’i suka gabatarwa babbar kotun Kaduna a matsayin hujjar neman bada belin sa cikin gaggawa.
A ƙunshin cajin da hukumar ta miƙa gaban babbar kotun birnin Tarayyar, ICPC na tuhumar farfesa Bello Abubakar da laifin amfani da takardar korarren likita da niyyar yaudarar Jama’a ta hanyar rubuta bayanan bogi game da bayanai da kuma yanayin ƙoshin lafiyar Nasiru El-Rufa’i, wadda ke tsare a hannun hukumar ta ICPC, lamarin da ta ce ya sabawa sashi na 17 (1) da (c) na kundin dokar yaki da rashawa ta shekara 2000.

NASIR EL-RUFAI YA NEMI AFUWA KAN KARAR DA ICPC TA SHIGAR A KANSA

Kazalika, hukumar ta ICPC na zargin cewa, Farfesa Bello Abubakar yayi amfani da matsayin sa mai daraja a fannin kiwon lafiya wato Babban likita da ake kira (Consultant), wadda al’umma ta aminta da ƙwarewarsa wajen rubuta wannan rahotan bogi tare da fitar da shi domin mikawa ga kotu, al’amarin da tace ya ci karo da sashi na 19 na kundin dokar penal code.
Haka kuma ICPC na tuhumar farfesa Bello Abubakar da amfani da takardar aiki mai ɗauke da tambari da hatimin Babban Asibitin Ƙasa na Abuja, domin damfarar kotun Kaduna ta bada belin Malam Nasiru El-Rufa’i, duk da cewa, yana sane cewa, bayanai da rahotan daya wallafa na bogi ne, lamarin da tace ya saba da tanadin kundin penal code sashi na 362 da 364.

Kano: An Soke Dokar Da Ta Kafa Hukumar KNUPDA – ‎Majalisar Dokoki ‎

A ranar juma’ar data gabata ne hukumar ta ICPC ta gurfanar da Babban likitan na tsohon gwamnan Kaduna bisa zargin waɗannan tuhume-tuhume guda 4 kuma nan da kwanaki masu zuwa ne ake sa ran Babbar Kotun  Birnin Tarayya ta Abuja zata sanya ranar fara sauraron shari’ar.

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You May Also Like

Lafiya

Daga Dr. Sunusi U. Na’ibi Yadda mutum ke wanke baki da kuma irin burushin da yake amfani da shi suna iya canza lafiyar baki...

Noma da Kiwo

DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA (2) Daga Yazid Sunusi YahayaRead also: DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA UKU (3)...

Noma da Kiwo

Dabarun kiwan kaji a lokacin yanayi na sanyi Daga Yazid Sunusi YahayaRead also: DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA UKU (3) Sau...

Kano

Gwamnatin Kano Ta ƘirƘiri Sabon Tsarin Biyan Fansho da Giratuti Ta Intanet Gwamnatin Jihar Kano ta ƙaddamar da wani sabon tsari na musamman na...