Fursunoni 61 Sun Haddace Alƙur’ani Mai Tsarki a Gidan Gyaran Hali na Kano
Daga Sunusi K/Naisa
Hukumar Gidan Gyaran Hali ta Ƙasa (NCoS) reshen Jihar Kano ta sake cimma wani gagarumin nasara a shirinta na gyaran hali da sauya rayuwar fursunoni, bayan da fursunoni 61 da ke Kurmawa, Kano, suka kammala haddace tare da sauke Alƙur’ani Mai Tsarki.
Read also: Tsohon ma’aikacin gidan rediyo Kano, Malam Ali Sufi Utai, ya rasu
Hukumar Shari’a ta Yi Wa Wasu Alƙalai da Ma’aikata Ritayar dole A Jihar Kano
Read also: Jami’in KAROTA Yayi Sanadin Kama Wani Da Ake Zargin Barawan Mota da Kuma Kungiyar Su A Kano
Wannan nasara ta nuna ƙudirin hukumar na ci gaba da aiwatar da shirye-shiryen gyaran hali, tarbiyya da kuma shiryar da fursunoni domin komawa cikin al’umma bayan kammala zaman hukuncinsu.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da Jami’in Hulɗa da Jama’a na Hukumar Gidan Gyaran Hali ta Kano, Musbahu Lawan K/Nassarawa, ya fitar ga manema labarai.
Sanarwar ta bayyana cewa wannan nasara ta nuna jajircewar hukumar wajen aiwatar da shirye-shiryen gyaran tarbiyya da koyarwar addini, daidai da tanade-tanaden Dokar Hukumar Gidan Gyaran Hali ta Najeriya ta shekarar 2019.
Ta ƙara da cewa shirin haddar Alƙur’ani na daga cikin manyan shirye-shiryen gyaran hali da hukumar ke gudanarwa domin gina tarbiyya, inganta ɗabi’u nagari da kuma shirya fursunoni su zama mutane masu amfani ga al’umma bayan fitowarsu daga gidan gyaran hali.
A cewarsa, cikin waɗanda suka kammala shirin akwai maza 55 da mata 6, waɗanda suka nuna jajircewa, haƙuri da ƙwazo tun daga farkon shirin har zuwa kammalawarsa. Ya ce abin farin ciki shi ne da dama daga cikinsu ba su da cikakkiyar masaniya kan karatun Alƙur’ani kafin shigarsu gidan gyaran hali.
Ya ce ta hanyar horo, jajircewa da kuma ingantaccen koyarwar addini, yanzu sun samu damar haddace Alƙur’ani Mai Tsarki gaba ɗaya.
Musbahu Lawan ya bayyana cewa hakan ya tabbatar da irin gagarumin tasirin da shirye-shiryen gyaran hali ta hanyar koyarwar addini ke da shi wajen sauya rayuwar fursunoni.
Ya kuma bayyana cewa domin karrama waɗanda suka kammala shirin, Hukumar Gidan Gyaran Hali ta Najeriya tare da haɗin gwiwar Gidauniyar Chokali Humanitarian Foundation sun rabawa waɗanda aka yaye kayan tallafi.
Gidauniyar ta bai wa kowane daga cikin waɗanda suka kammala shirin sabbin kaya, katifa, bargo da kuma tallafin kuɗi domin ƙarfafa musu gwiwa wajen ci gaba da kyautata rayuwarsu da kuma sauƙaƙa musu komawa cikin al’umma.
Kwanturolan Hukumar Gidan Gyaran Hali na Jihar Kano, Ahmed Yusuf Lakpene, ya yabawa Babban Kwanturolan Hukumar Gidan Gyaran Hali ta Ƙasa, Sylvester Ndidi Nwakuche, bisa jagoranci nagari da kuma ci gaba da ba da umarnin aiwatar da shirye-shiryen ilimi, koyon sana’o’i da gina ɗabi’a a cibiyoyin gyaran hali na faɗin ƙasa.
Ya ce irin waɗannan shirye-shirye na taka muhimmiyar rawa wajen bai wa fursunoni ilimi, ƙwarewa da kyawawan ɗabi’u domin su zama ‘yan ƙasa nagari masu anfani ga al’umma bayan fitowarsu.
Jami’in da ke kula da Gidan Tsaro Masu Matsakaicin Tsaro na Kurmawa, DCC Ibrahim Isah Rambo Ibrahim, ya gode wa Hukumar Gidan Gyaran Hali ta Kano da kuma Gidauniyar Chokali Humanitarian Foundation bisa irin goyon bayan da suke bai wa shirin.
Ya bayyana bikin saukar Alƙur’anin a matsayin shaida ta kyakkyawan jagoranci, haɗin kai da kuma jajircewar hukumar wajen tabbatar da cikakken gyaran hali ga fursunoni.
Da yake jawabi a wajen taron, Farfesa Aliyu Harun ya yabawa hukumar bisa ci gaba da gudanar da shirye-shiryen da ke sauya rayuwar fursunoni ta hanyar ingantattun shirye-shiryen gyaran hali.
Ya jaddada cewa irin waɗannan shirye-shirye na taimakawa wajen mayar da fursunoni mutane nagari masu bin doka da oda.
Read also: Hukumar Shari’a ta Yi Wa Wasu Alƙalai da Ma’aikata Ritayar dole A Jihar Kano
Ƙungiyar PTA First Lady College Ta Yi Allah-Wadai Da Bikin ‘Candy’ Ta Buƙaci Ɗaukin Gwamnati
A nata jawabin, Shugabar Kwamitin Yafe wa Masu Laifi na Jihar Kano, Hajiya Azumi Namadi Bebeji, ta sake tabbatar da aniyar Gwamnatin Jihar Kano na ci gaba da inganta walwalar fursunoni.
Ta yabawa Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, bisa tausayi da kuma ci gaba da tallafa wa fursunoni a cibiyoyin gyaran hali da ke jihar.
Shi kuma Shugaban Kwamitin Shirya Taron, CSC Mohd Ali Kibiya, ya taya fursunoni 61 da suka kammala shirin murnar wannan gagarumar nasara.
Ya buƙace su da su ci gaba da riƙo da tarbiyya, kyawawan ɗabi’u da ci gaban ruhaniya da suka samu yayin shirin, tare da ƙarfafa sauran fursunoni su ci gaba da yi wa Najeriya addu’ar samun zaman lafiya, haɗin kai da ci gaba mai ɗorewa.
An kammala taron da addu’o’i na musamman da Limamin Kiristoci na gidan gyaran hali, DSC Mohd Alkanawy, da Babban Limami, Imam Nasiru Abdu, suka jagoranta domin yi wa fursunoni, Hukumar Gidan Gyaran Hali ta Najeriya, Jihar Kano da kuma ƙasa baki ɗaya addu’ar samun zaman lafiya da ci gaba.
Hakimin Dan Ruwatan Kano, Alhaji Ibrahim Ado Bayero, ya miƙa takardun shaidar kammala haddar Alƙur’ani ga fursunoni 61 a yayin taron.
Hukumar Gidan Gyaran Hali ta Najeriya reshen Jihar Kano ta sake jaddada aniyarta na ci gaba da aiwatar da shirye-shiryen gyaran hali, ilimi, koyon sana’o’i, tarbiyya da koyarwar addini domin sauya rayuwar fursunoni, inganta tsaron al’umma da kuma bayar da gudunmawa ga ci gaban ƙasa.




























