Gwamna Yusuf Ya Umarci a Binciki Tsohon Shugaban Ma’aikata Abdullahi Musa Kan Zargin Badakalar ₦1.5bn
Daga Sunusi K/Naisa
Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya bayar da umarnin gudanar da bincike kan zargin cire Naira biliyan 1.5 daga albashin ma’aikata, wanda ake dangantawa da tsohon Shugaban Ma’aikatan Jiha, Abdullahi Musa.
Read also: Hukumar Shari’a ta Yi Wa Wasu Alƙalai da Ma’aikata Ritayar dole A Jihar Kano
Yusuf ya bayar da wannan umarni ne a ranar Juma’a yayin bikin Ranar Ma’aikata ta Duniya ta shekarar 2026 da aka gudanar a filin wasa na Sani Abacha da ke Kano.
Gwamnan ya bayyana cewa binciken zai mayar da hankali ne kan zarge-zargen da suka shafi tsohon Shugaban Ma’aikatan.
“Bayan zargin cire Naira biliyan 1.5 daga albashin ma’aikata da ake yi wa tsohon Shugaban Ma’aikatan, ina bayar da umarnin a gudanar da bincike kan wannan zargi da gaggawa,” in ji Yusuf.
Ya kuma tabbatar wa ma’aikata cewa duk wanda aka samu da laifi zai fuskanci hukunci da ya dace, ya ƙara da cewa duk kuɗin da aka kwato za a mayar wa ma’aikatan da abin ya shafa.
“Wannan gwamnati taku ce kuma za ta yi aiki tare da ku. Abin da take buƙata daga gare ku shi ne goyon baya da jajircewa wajen aiki,” in ji gwamnan.
Haka kuma Yusuf ya sake jaddada kudirin gwamnatinsa na biyan basussukan kuɗaɗen waɗanda suka bar aiki (gratuity) da haƙoƙin waɗanda suka mutu da ake bin gwamnati ga masu a jihar.
A cewarsa, gwamnatin ta riga ta biya Naira biliyan 32 daga cikin Naira biliyan 48 da ta gada daga gwamnatin da ta gabata, tare da alƙawarin kammala biyan sauran Naira biliyan 16 kafin ƙarshen wa’adin gwamnatin sa a shekarar 2027.
Tun da fari, Shugaban Kungiyar Ƙwadago ta Najeriya (NLC) reshen Jihar Kano, Kabir Inuwa, ya yaba wa gwamnatin jihar kan biyan albashi da kuma hakkokin masu ritaya.
Read also: Shugaban ‘Yan Bindiga Bello Turji Na yunƙurin Miƙa Wuya Bayan Mutuwar Yelo Danbokolo
Sai dai ya buƙaci gwamnan da ya magance bambancin albashi tsakanin ma’aikatan jiha da na ƙananan hukumomi.
Inuwa ya kuma yi kira da a gudanar da cikakken bincike kan zargin cire Naira biliyan 1.5 daga albashi tare da dawo da kuɗin idan aka tabbatar da zargin.




























