Karo na Biyu: Kimanin Kayan Abinci na Sama da Naira miliyan 42 aka Rabawa Kungiyoyi a jihar Kano
Daga Yazid Sunusi Yahaya
Read also: One Kano Agenda: Gwamna Yusuf Ya Nuna Samun Haɗin Kai Shine Mabuɗin Farfaɗo da Jihar Kano
A ci gaba da rabon tallafin kayan abinci ga ƙungiyoyi a jihar Kano, a kashi na biyu, an raba kayan abinci da kuɗi wanda jimlar su bai gaza Naira Miliyan Arba’in da Biyu (₦42 miliyan) ba, a karo na biyu a ranar Talatar nan.
Taron wanda aka gabatar da shi a gidan gwamnatin Kano, ƙarƙashin jagorancin Gwamnan Abba Kabir Yusuf, ya samu halartar wasu Kwamishinonin da Shugaban Jam’iyyar APC na Jiha Kano, Alhaji Umar Haruna Doguwa, tare da masu bai wa Gwamna shawara da shugabannin sassan gwamnati, da kuma masu shirya fina-finan Hausa.
Da yake jawabi Gwamnan Abba Kabir Yusuf Ya Yabawa Kwamishinan Ma’aikatar Kasa da Tsare-tsare bisa hangen nesa na tallafawa Kungiyoyin dake Jihar Kano da kayan abinci da kuma kuɗin chefane domin faranta wa al’umma musamman a wannan wata Mai alfarma na Ramadan.
Shugaba Tinubu ya Amince da Ranakun Hutun Sallah Ƙarama
Read also: Wasu Ma’aikatun Gwamnati Zasu Sami Sabbin Shugabanni A Kano
Gwamnan, wanda ya samu wakilcin Mai bashi Shawara kan Harkokin Siyasa, Alhaji Hamza Buhari Ba Kwana, ya jinjina wa Kwamishinan Ma’aikatar Kasa da Tsare-tsare, Abduljabbar Muhammad Umar, wanda shi ya ƙirƙiri shirin da niyar ragewa jama’a raɗaɗɗen rayu a daidai wannan lokaci da ake da matsananciyar bukata.
Ya yabawa kokarin Kwamishinan kan ayyukan alkhairi da yake gudanarwa, yana mai jaddada cewa irin waɗannan shirye-shirye na taimakawa wajen inganta rayuwar al’umma. Ya kuma tabbatar da cewa ya zuwa wanna rana, wato Talata, an raba kayan abinci da kuɗaɗen su bai ƙasa da Naira miliyan 42 ba.
Ya bada tabbacin gwamnatin su zata ci gaba da farantawa al’umma tare da samar musu ababen more rayuwa, ya bada misali da ayyukan raya kasa, kamar gina hanyoyi da samar da hasken lantarki da tallafawa ilimi da makamantansu.
A nasa jawabin, Kwamishinan Ma’aikatar Kasa da Tsare-tsare, Abduljabbar Muhammad Umar, ya bayyana jin daɗinsa kan yadda aka gudanar da taron na rana ta biyu, inda aka raba kayan abinci da kuɗaɗe ga kungiyoyin al’umma da na jam’iyya domin tallafa musu.
Kwamishina yayi fatan jama’ar jihar Kano zasu ci gaba da yiwa gwamnatin Abba gida-gida addu’a da kuma bata goyan baya domin ciyar da Kano gaba.
Kungiyoyin da suka ci gajiyar shirin a wannan lokaci sun haɗar da Beneficiaries APC Media Forum da APC Marshalls da APC Youth & Women da Kano First Movement da Abba Door to Door da kuma Kannywood.
Read also: Auren Gata Da Gwamnatin Kano Ta Yi Haramun Ne, Inji Sheik Hadi MaiHula
Tsaro: Hukumar Yan sanda ta Haramta Yin Wasan Tashe
Idan za a tuna a ranar Litinin da ta gabata aka ƙaddamar da rabon kayan abinci ga ƙungiyoyi addini da kuma na ci gaban al’umma daban-daban.




























