Kwankwaso Ya Bada Sabbin Muƙamai Ga Kwamishinonin da Suka Bar Kujerunsu Don Ɗabbaƙa Shahadar Kwankwasiyya
Daga Sunusi K /Naisa
Read also: Rashin Kulawa Na Daga Cikin Bukatun Da Matar Gwamna Abba Ta Kai Kara A Kotu Don A Raba Su
Jagoran ɗarikar Kwankwasiyya, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya amince da naɗa tsofaffin kwamishinonin Jihar Kano da suka biyo bayansa sabbin muƙamai a cikin shugabancin ƙungiyar.
Sanarwar ta fito daga Mai taimaka wa tsohon Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso kan yaɗa labarai, Saifullahi Hassan, a ƙarshen mako.
Sanarwar ta ce an naɗa tsohon Kwamishinan Tsaro, AVM Ibrahim Umaru, a matsayin Babban Jami’in Tsaro na tafiyar Kwankwasiyya, a inda tsohon Kwamishinan Kimiyya da Fasaha, Dakta Yusuf Kofar Mata, aka naɗa shi Sakataren Kwamitin Dattijan Kwankwasiyya na Jiha.
Read also: “Ku Bar Ofisoshi Ko Ku Fuskanci Hukunci,” Gwamnatin Kano Ta Gargadi Ma’aikatan Da Suka Kai Ritaya
Biyan Ƴan Fansho Haƙƙin su Shine Muhimmi Akan Bawa Malamai da Fasto Hasafi, In ji Kwamrade Alhassan
Haka kuma tsohon Kwamishinan Ayyuka na Musamman, Alh. Nasiru Sule Garo, ya samu muƙamin Sakataren CRC. Shi kuwa tsohon Mai Bai wa Gwamna Shawara kan Harkokin Siyasa, Alh. Sanusi Surajo Kwankwaso, ya zama Daraktan Wayar da Kan Jama’a na ƙungiyar.
Sauran waɗanda aka naɗa sun haɗar da tsohon Kwamishinan Jin Kai, Alh. Adamu Kibiya, wanda ya zama Sakataren Kano PROPA, tsohon Kwamishinan Matasa, Mustapha Rabi’u Musa, an ba shi muƙamin Sakataren ƙungiyar Kwankwasiyya baki ɗaya.
Gwamna Abba Kabir Yusuf Ya Dongwarar da Jam’iyyar NNPP
Sanarwar ta bayyana cewa waɗannan naɗe-naɗe an yi su ne domin ƙarfafa tsarin jagoranci da kuma inganta haɗin kai a tsakanin mambobin ƙungiyar. Ana sa ran sabbin jami’an za su yi amfani da kwarewar su wajen ciyar da manufofin tafiyar gaba a dukkan matakai.




























