Biyan Ƴan Fansho Haƙƙin Shine Muhimmi Akan Bawa Malamai da Fasto Hasafi, In ji Shugaban Kungiyar
Daga Muazu Hardawa Bauchi
Read also: One Kano Agenda: Gwamna Yusuf Ya Nuna Samun Haɗin Kai Shine Mabuɗin Farfaɗo da Jihar Kano
Read also: Rashin Kulawa Na Daga Cikin Bukatun Da Matar Gwamna Abba Ta Kai Kara A Kotu Don A Raba Su
Shugaban Ƙungiyar ‘Yan Fansho ta Ƙasa (NUP), reshen Jihar Bauchi, Comrade Abdullahi Al-Hassan Misau, ya bayyana cewa ‘yan fansho su ne ke da haƙƙi na kai tsaye a kan gwamnati fiye da malamai, ko pastoci a fannin kyautatawa ko sauke nauyi.
Comrade Abdullahi Al-Hassan ya yi wannan bayani ne yayin da yake tsokaci kan shawarwarin da ake yi ko aka yanke na fara biyan malaman addini kuɗaden alawus da gwamnatin jihar Bauchi ta sanar za ta ci gaba da yi.
Ya ce “Malamai da limamai da pastoci duk suna yin addini saboda Allah ne kuma baza su so a tauye hakkin masu hakki a hana kudin barin aiki da fansho, su kuma a cika musu aljifan su ba.”
Kwamared Abdullahi Misau ya ce tun a baya, al’ummar gari ne ke tallafa wa malaman addini ba tare da gwamnati ta shiga tsakani ba. Amma a yanzu duk taimakon da gwamnatin ke musu ana ganin ana yi ne don a toshe bakin su daga fada wa shugabannin gwamnatin gaskiya don su gyara kura kuran su ba.
Read also: Kano: An Soke Dokar Da Ta Kafa Hukumar KNUPDA – Majalisar Dokoki
Ana Zargin Batagarin Matasa Da Bankawa Dubban Kaburbura Wuta A Makabartar Turum Dake Bauchi
Shugaban NUP ya jaddada cewa biyan malamai ba ya cikin wajibcin gwamnati.illa gani ake yi toshiyar baki ke don hana su fadar gaskiya. Madadin bin wannan hanya ta basu kudi haka siddan, ya kamata a fito da dokar da za ta tsara musu wani aiki da zai taimaki mutane a hukuma ce kamar yadda suke yin adduah.
Ya kara da cewa ba haƙƙin gwamnati ba ne, ta rika biyansu kwasar kudi tana ba su ba tare da tsara kaidar doka da za ta kwantar musu hankali su san cewa duk abin da aka ba su halas ne ba.
Kwamared Abdullahi Misau ya ce ‘yan fansho sun yi hidima wa gwamnati tsawon shekaru, don haka su ne suka fi cancantar a kula da su a basu hakkin su don lura da Jan su da Iyalan su da kuma lafiyar su a lokacin da suka wahala yin aiki wa gwamnati karfin su ya kare.
“Mu ‘yan fansho mun bauta wa gwamnati, mun tsufa a cikinta, ƙarfin mu ya ƙare. Wasu ma a cikin aiki ne suka samu lalura aka tilasta musu yin ritaya, amma kullum sune cikin wahala.” inji Kwamared Abdullahi Misau.
Ya ƙara da cewa bai dace a fifita wasu bangarori a bar ‘yan fansho cikin wahala ba, alhali mutanen su su ne ke da haƙƙi na gaskiya a wajen gwamnati, ba malamai da pastoci ko limamai ba, da ake ganin suna yiwa kasa adduah ba.
Suma Idan suka yi adduah a matsayin masu hakkin da aka tauye, Allah zai bi musu kadi ya saka musu. Cin zarafi da tauye hakkin masu hakki ke jefa kasar cikin matsalar rayuwa.
Don haka ya bukaci Gwamna Bala Mohammed Abdulkadir ya tuna alkawarin da ya yi wa maaikata na biyan su harkokin su tun a lokacin kamfen kafin ya hau kujerar Gwamna amma har yanzu ya kasa cikawa.
Kishin Bunƙasar Kano Shi Yasa Gwamna Yusuf Ya Yi Sauyin Sheka – NNPP
Ya ce Gwamna Bala Mohammed ya tuna cewa tsohon maaikaci babu abin da za ka masa ka burge shi.wanda ya wuce ka biya shi kudin ritaya na giratuti ka ba shi fansho mai ingancin da aka tanada masa don ya lura da kansa har ya koma ga Allah saboda aiki wa gwamnati ya cinye masa karfi.




























