Saudiyya ta sanar da ganin watan Ramadan
Daga TSN Hausa
Read also: Rashin Kulawa Na Daga Cikin Bukatun Da Matar Gwamna Abba Ta Kai Kara A Kotu Don A Raba Su
Hukumomin ƙasar Saudiyya sun umurci a fara azumi daga gobe Labaraba, 18 ga watan Fabareru na 2026, wanda ya yi dai-dai da 1 ga watan Ramadan 1447.
A yau Talata ne rahotanni ke cewa an ga jinjirin watan azumin Ramadan a sassa daban-daban na ƙasar Saudiyya.
Read also: EFCC Ta Kori Ma’aikata Sama da 40, Ta Gurfanar da Biyar Kan Cin Hanci da Rashawa
Hukumomi sun umurci a fara azumi daga gobe Laraba.
Shafin Haramain Sharifain ne ya ruwaito hakan, inda ya ce, “an ga jinjirin watan Ramadan na shekarar 1447 wato shekarar 2026 a Saudiyya.
Tunda farko babbar kotun Ƙolin Saudiyya ce ta yi kira ga dukkan Musulmi a faɗin ƙasar da su fita domin neman jinjirin watan Ramadan a yammacin ranar Talata, 29 Sha’aban 1447AH, daidai da 17 ga Fabrairu, 2026 bisa kalandar Umm Al-Qura.
Read also: Gwamnatin Kano Ta Sanar da Hutun Bikin Takutaha
Biyan Ƴan Fansho Haƙƙin su Shine Muhimmi Akan Bawa Malamai da Fasto Hasafi, In ji Kwamrade Alhassan
Sanarwar ta kara da cewa za’a fara Sallar Asham a ƙasar musamman masallacin Ka’aba da ke Mecca da na Madina wato Masallacin Annabi Muhammad SAW.



























