Rigimar Masarautar Kano Na Daf Da Zama Tarihi, In Ji Kwamishina Waiya
Daga Wakilinmu
Read also: Kano: An Soke Dokar Da Ta Kafa Hukumar KNUPDA – Majalisar Dokoki
Read also: Fursunoni 61 Sun Haddace Alƙur’ani Mai Tsarki a Gidan Gyaran Hali na Kano
Gwamnatin Jihar Kano ta ce rikicin da ya daɗe yana gudana kan masarautar Kano zai zo ƙarshe cikin lumana nan ba da jimawa ba.
Kwamishinan Yaɗa Labarai da Harkokin Cikin Gida, Ibrahim Abdullahi Waiya, ne ya bayyana hakan yayin da yake zantawa da manema labarai a ranar Alhamis a Kano.
Waiya ya tabbatar wa al’ummar jihar cewa tuni aka ɗauki matakai na gaskiya domin dawo da zaman lafiya da kwanciyar hankali mai ɗorewa a Kano.
Ya ce gwamnatin jihar ta ƙudiri aniyar tattaunawa da dukkan masu ruwa da tsaki, yana jaddada cewa gwamnatin ta himmatu wajen tabbatar da cewa batun masarautar ba zai ci gaba da haifar da tashin hankali ko kawo cikas ga gudanar da mulki ba.
A cewarsa, tsarin da gwamnati ke bi yana ƙarƙashin girmama bin doka da oda, darajar cibiyoyin gargajiya, da kuma muradun bai ɗaya na al’ummar Jihar Kano.
Read also: Gobara : Kasuwar Ƴan Katako A Kano Ta Kama da Wuta
Kishin Bunƙasar Kano Shi Yasa Gwamna Yusuf Ya Yi Sauyin Sheka – NNPP
Idan za tuna an naɗa Sarki Muhammadu Sanusi II a matsayin Sarkin Kano na 16 a watan Mayun 2024, bayan cire Sarki Aminu Ado Bayero daga sarautar Kano da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya yi.
Gwamna Yusuf ya mayar da Sanusi II kan karagar sarauta nan take bayan ya rattaba hannu kan Dokar Soke Majalisar Masarautun Jihar Kano (Repeal) ta 2024.
Sabuwar dokar ta maye gurbin Dokar Majalisar Masarautun Jihar Kano ta 2019, tare da rusa majalisun masarautu da tsohon gwamnan jihar, Dr Abdullahi Umar Ganduje, ya kafa.
Dangane da sauya sheƙar Gwamna Abba Yusuf zuwa jam’iyyar All Progressives Congress (APC), kwamishinan ya bayyana matakin a matsayin wani ci gaba da zai kawo gagarumin alheri ga jihar.
Ya ce al’ummar Kano za su sa ran samun ƙarin ribar dimokiraɗiyya, inda ya jaddada cewa kusantar gwamnati da ta tarayya za ta jawo ƙarin tsoma baki, ayyuka, da shirye-shiryen ci gaba zuwa jihar.
“Sauya sheƙar ta buɗe ƙofofi da dama ga Kano. Tare da ƙarfafa haɗin gwiwa da Gwamnatin Tarayya, muna sa ran samun ƙarin tallafi a muhimman fannoni kamar ababen more rayuwa, lafiya, ilimi, da jin ƙai na zamantakewa,” in ji Waiya.
Dangane da makomar siyasar Mataimakin Gwamna wanda bai sauya sheƙa tare da Gwamnan ba, kwamishinan ya ce wannan shawara ta mutum ce kai tsaye.
Ya bayyana cewa yana hannun Mataimakin Gwamna ya yanke shawarar ko zai ci gaba da aiki tare da Gwamnan a sabon tsarin siyasa ko kuma ya zaɓi wata hanya dabam.
Waiya ya jaddada cewa gwamnatin jihar na ci gaba da mai da hankali kan mulki nagari, haɗin kai, da ci gaba, tare da kira ga al’ummar Kano da su zauna lafiya su kuma ba da goyon baya yayin da ake ci gaba da ƙoƙarin warware batutuwan da suka rage da kuma tura jihar gaba.
Gwamna Abba Kabir Yusuf Ya Dongwarar da Jam’iyyar NNPP
Ya sake tabbatar da ƙudurin gwamnatin na gaskiya, zaman lafiya, da mulki mai haɗa kowa da kowa, yana mai tabbatar da cewa muradun al’ummar Kano za su kasance a gaba ko da yaushe. (NAN)




























