EFCC ta Gurfanar Da Ɗan Austria Kan Boye Bayyana Wasu Maƙudan Kuɗaɗe $800,575 da €651,505
Daga Yazid A Yahaya
Read also: Kwamiti Ya Kama Jabiru Sanda Zage da Kwalaben Kodin 151 a Kano, Ya Fuskanci Hukunci Kotu
Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa da Laifukan Tattalin Arziki Ƙasa (EFCC) ta gurfanar da wani ɗan ƙasar Austria mai suna Kavlak Onal a gaban Kotu sakamakon samun sa dauke da maƙudan kuɗaɗe wanda bai gabatar da bayyana su ba.
Onal an chafke shi a filin jirgin saman Legas da yake ƙoƙarin hawa jirgin Emirates Airline zuwa Dubai.
Daraktan shiyya na biyu na Hukumar EFCC a Legas, ya gurfanar da Kavlak Onal a gaban Mai Shari’a Yelim Bogoro na Babbar Kotun Tarayya reshen Legas, a ranar Juma’ar data gabata.
An kama Onal a filin jirgin saman Legas ne daga hannun Hukumar Kwastam ta Nijeriya (NCS) bisa zargin gaza bayyana mallakar $800,575 da €651,505 da ke tare da shi. Ana sa ran zai tashi ta jirgin Emirates zuwa Dubai, sai jami’an Kwastam suka tare shi yayin bincike na yau da kullum a teburin bayyana kuɗaɗen waje (AML/CFT Currency Declaration Desk) a ranar 16 ga Disamba a Filin Jirgin Sama na Murtala Muhammed, Legas.
Read also: HUKUMAR ICPC TA GURFANAR DA LIKITAN NASIRU ELRUFAI A GABAN KOTU
Daga nan aka miƙa shi ga EFCC domin ci gaba da zurfafa bincike.
Bayan kammala bincike, an gurfanar da wanda ake tuhuma a ranar 9 ga Janairu kan tuhume-tuhume biyu na safarar kuɗaɗen haram (money laundering).
A tuhuma ta farko an ce: “Cewa kai, Mr. Kavlak Onal, a ranar 13 ga Disamba, a Legas, cikin ikon wannan kotu, ka gaza bayyana adadin $800,575 (Dala dubu dari takwas da dubu dari biyar da saba’in da biyar) ga Hukumar Kwastam ta Nijeriya a Filin Jirgin Sama na Murtala Mohammed, Ikeja, Legas, don haka ka aikata laifi da ya saɓa wa doka ƙarƙashin Sashe na 3(5) na Dokar Hana fatauci da hada-hadar kuɗi ta haram da wanke Kuɗi, 2022.”
Kavlak Onal, ya ce “ba ni da laifi” ga dukkan tuhume-tuhumen da aka karanta kuma ake zargina da su”. Don haka yake roƙon Kotu ta sake shi.
lauyan gwamnati Bilikisu Bala Buhari ta roƙi kotu ta sa ranar shari’a domin gwamnati ta gabatar da hujjoji, tare da neman a tsare wanda ake tuhuma a gidan gyaran hali.
Read also: Kotun Tarayya a Gombe Ta Soke Zaben da Aka Yiwa Farfesa Isa Ali Pantami
Sojoji Sun Daƙile Hari Yan Bindiga A Kano
Lauyan kariya, Stanley Imhanruor, ya sanar da kotu cewa ya shigar da buƙatar beli a madadin wanda yake karewa.
A martani, lauyar gwamnati ta ce an ba ta kwafin buƙatar belin da ƙarfe 9:07 na safe a ranar 9 ga Janairu, kuma tana buƙatar lokaci domin amsawa.
Saboda haka, Mai Shari’a Bogoro ya ɗage shari’ar zuwa 16 ga Janairu domin sauraron buƙatar belin, kamar yadda kakakin EFCC, Dele Oyewale, ya bayyana.



























