Connect with us

Hi, what are you looking for?

Labarai

Kano Online Media Chapel ta yabawa kamfanonin Dala Food Nig da POP Cola

POP cola Dala food
POP cola Dala food

Kano Online Media Chapel ta yabawa kamfanonin Dala Food Nig da POP Cola

Daga Yazid Sunusi Yahaya

Kungiyar yan jaridun yanar Gizo ta ƙasa reshen jihar kano, Online Media Chapel ta yabawa kamfanin Dala Food Nig limited da Kamfanin POP Cola, bisa irin girmamawa da karramawar da kamfanonika suka yi wa kungiyar, a yayin taron ƙarawa mambobinta ilimi da sanin makamar aiki ta yadda za su koyi amfani da fasahar AI.

Shugaban ƙungiyar Abubakar Abdulƙadir Dangambo ne ya bayyana haka, yayin gudanar da taron a ranar Talata a dakin taro na Ma’aikatar sufuri ta jihar Kano.

Rashin aikin yi: Ɗalibai a Najeriya sun fara sauya tunani daga karatu zuwa ilimin koyan sana’a – Dr. Auwal Amba

Kamfanin Dala Food Nig limited sun turo ma’aikatan su, inda suka dama kunun tsamiya aka rabawa mahalarta taron cikin girmamawa, manyan baƙi da kananan kowa ya yaba da kunun.

Su kuma kamfanin POP Cola sun samar da lemuka da ruwa wadatattu a wajen turon kyautata don ƙara kyautata dangantakar da ke tsakanin kamfanonin biyu da kungiyar.

Dangambo ya ƙara yabawa kamfanunuwan duba da yadda aka tura musu buƙatar hakan a kurenren lokaci, kuma suka amince suka zo wajen taron da kayayyakin nasu.

A ƙarshe Abubakar Dangambo ya yi musu fatan alheri da kasuwa mai albarka cikin harkokin su ya kuma ce ƙungiyar zata ci gaba da ɗorewa da kyakkyawar hulda da ke tsakanin su.

Yadda Laftanar AM Yarima ya tsallake harin ‘yan bindiga

Idan za a tuna a ranar Laraba 18 ga watan Nuwamba na wannan shekara, Ƙungiyar yan jaridun yanar Gizo ta ƙasa reshen jihar kano ta gabatar da taron ƙarawa juna sani ga mambobinta a cikin babban birnin jihar Kano.

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You May Also Like

Lafiya

Daga Dr. Sunusi U. Na’ibi Yadda mutum ke wanke baki da kuma irin burushin da yake amfani da shi suna iya canza lafiyar baki...

Noma da Kiwo

DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA (2) Daga Yazid Sunusi YahayaRead also: DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA UKU (3)...

Noma da Kiwo

Dabarun kiwan kaji a lokacin yanayi na sanyi Daga Yazid Sunusi YahayaRead also: DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA UKU (3) Sau...

Kano

Gwamnatin Kano Ta ƘirƘiri Sabon Tsarin Biyan Fansho da Giratuti Ta Intanet Gwamnatin Jihar Kano ta ƙaddamar da wani sabon tsari na musamman na...