Fitaccen ɗan jarida Aliyu Abubakar Getso ya rasu
Daga Sunusi K/Na’isa
Fitaccen ɗan jarida kuma masani a fagen yaɗa labarai, Malam Aliyu Abubakar Getso, ya rasu da safiyar Lahadi a birnin Kano.
Rahotanni daga Nigerian Tracker sun tabbatar da cewa za a gudanar da sallar jana’izarsa a gidansa da ke Janbulo, cikin birnin Kano.
Read also: Ansamu Koma Bayan ‘Yancin Gudanar Da Aikin Jarida a Faɗin Duniya A Shekaru 5 – Rahoton IEAD
Marigayi Getso ya shafe shekaru da dama yana aikin jarida, inda ya yi aiki a Ma’aikatar Yaɗa labarai ta jiha da manyan gidajen rediyo da dama a Kano, ciki har da Radio Kano, Freedom Radio, Vision FM, da Premier Radio, inda ya taka muhimmiyar rawa a fannin editing da fassarar labarai.Haka kuma Getso ya taba zama Sakataren yan jaridu da Kungiyar Kwadago na jihar Kano.
Read also: Tsohon ma’aikacin gidan rediyo Kano, Malam Ali Sufi Utai, ya rasu
Aliyu Getso ya kasance ɗaya daga cikin fitattun masu ba da gudummawa wajen bunƙasa aikin jarida a Kano da ma Arewa gaba ɗaya. Abokan aikinsa da dama sun bayyana rasuwarsa a matsayin babban rashi ga masana’antar yada labarai a Najeriya.
Allah Ya jikansa da rahama, Ya ba iyalansa da abokan aikinsa haƙuri da juriya.



























