Connect with us

Hi, what are you looking for?

Lafiya

Ƙungiyar likitoci ta janye yajin aikin gargaɗin da ta fara

Likitoci
Likitoci

Daga Sunusi K/Na’isa
A taimaka da yaɗa Labarin

Shugaban ƙungiyar likitoci masu neman ƙwarewa ta Najeriya, Dakta Tope Osundara, ya bada sanarwar janye yajin aikin da ƙungiyar ta fara na gargaɗi a kwana biyu da fara.

Shugaban ya sanar da haka a wani saƙo da ya aika wa jaridar Punch da ake wallafawa a daren ranar Asabar 13 ga watan Satumbar, 2025, inda ya umarci mambobinsu da su koma bakin aiki a yau Lahadi.

Osundara, yace sun janye yajin aikin ne sakamakon gwamnati ta biya musu wasu daga cikin buƙatunsu, tare kuma da alƙawarin duba sauran batutuwan da suke yajin aiki akai.
Ƙungiyar ta kuma sake ba wa Gwamantin Tarayyar wa’adin wasu makwanni biyun da ta cika alƙawarin da ta ɗauka na biya musu sauran buƙatunsu, in ba haka ba za su tsunduma wani sabon yajin aikin. Kawo ya zuwa haɗa wannan rahoton babu wani ƙarin bayani game da buƙatun da aka biya wa yayen ƙungiyar.

A daren juma’ar da ta gabata ne likitocin masu neman ƙwarewa suka tsunduma yajin aikin na gargaɗi, bayan ƙarewar wa’adin da ƙungiyar ta ba gwamnatin tarayya kan batutuwan da suka shafi albashi, alawus, da walwalar ma’aikata.

Idan za a tuna a baya, ƙungiyar likitocin masu neman ƙwarewa NARD, ta ba wa Gwamnatin Tarayyar Najeriyar, wa’adi a mabanbantan lokuta kafin shiga yajin aikin na gargaɗi a ranar Juma’a.

Ƙarin Wani Labarin: SUBEB DA UNICEF DA UBEC SUN KADDAMAR DA GANGAMIN SA YARA MAKARANTA A BAUCHI 

Da farko sun ba ta wa’adin kwanaki 21 a watan Yulin da ya gabata, suka sake ba ta wani wa’adin na kwanaki 10 wanda ya ƙare a ranar 10 watan Satumbar nan, sai kuma wa’adin sa’o’i 24 da suka sake ba wa Gwamnatin gabanin shiga yajin aikin da suka kawo ƙarshensa a wannan Lahadi.

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You May Also Like

Lafiya

Daga Dr. Sunusi U. Na’ibi Yadda mutum ke wanke baki da kuma irin burushin da yake amfani da shi suna iya canza lafiyar baki...

Noma da Kiwo

DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA (2) Daga Yazid Sunusi YahayaRead also: DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA UKU (3)...

Noma da Kiwo

Dabarun kiwan kaji a lokacin yanayi na sanyi Daga Yazid Sunusi YahayaRead also: DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA UKU (3) Sau...

Kano

Gwamnatin Kano Ta ƘirƘiri Sabon Tsarin Biyan Fansho da Giratuti Ta Intanet Gwamnatin Jihar Kano ta ƙaddamar da wani sabon tsari na musamman na...