Connect with us

Hi, what are you looking for?

Labarai

Ranar Takuttaha: Rana ce ta Yawaita Adduo’i da Salati Ga Fiyayyen Halitta S.A.W- Shugaban Karamar Hukumar Dambatta

Shugaban Ƙaramar hukumar Danbatta
Shugaban Ƙaramar hukumar Danbatta

Ranar Takuttaha: Rana ce ta Yawaita Adduo’i da Salati Ga Fiyayyen Halitta S.A.W- Shugaban Karamar Hukumar Dambatta.

Uba Abdullahi

An bayyana ranar bikin Takuttaha da cewar rana ce ta yawaita istigifari da yawaita Salati ga Shugaban Halitta Annabi Muhammadu Sallalahu Alaihi Wa’ahlihi Wasallam, musamman ma bisa wannan biki na bana da ya kama a ranar Juma’a mai albarka tare da gudanar da adduo’i domin neman taimakon Allah S W.T akan matsalolin da al’umma su ka tsinci kansu a ciki da ƙasa baki ɗaya.

Wannan kira na kunshe ne a cikin wata tattaunawa da Shugaban Karamar Hukumar Dambatta Hon Jamilu Abubakar Dambatta ya yi da yan Jaridu a fadar Gwamnatin Jihar Kano jim kadan bayan ayyana yau Juma’a a matsayin ranar hutu da Gwamnan Jihar Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf ya yi domin tunawa da Ranar Takutaha ta bana.

A Karanta Wanna:BUƊAƊƊIYAR WASIKA ZUWA GA MAI GIRMA GWAMNAN JIHAR KANO, ENGR. ABBA KABIR YUSUF, DANGANE DA TSARIN TAIMAKEKENIYAR LAFIYA NA JIHAR KANO (KSCHIMA)

Hon. Jamilu Abubakar Dambatta ya ce ” Watan Rabi’ul Auwal wanda ake gabatar da Mauludi wata ne mai Daraja da Alfarma domin a irin wannan watan ne aka Haifi Fiyayyen Halitta Annabi Muhammadu Sallalahu Alaihi Wa’ahlihi Wasallam inda ya yi kira ga al’ummar Musulmi da su himmatu matuka wajen yawaita Salati ga Annabin Rahama S.A.W a wannan lokaci tare da kyautata adduo’i ga Allah Subhanahu Wata’ala domin kawo mana ɗauki daga cikin matsalolin da mu ka sami kanmu a ciki.”

Shugaban Karamar Hukumar ta Dambatta ya tunatar da ƙungiyoyin addini musamman ƙungiyoyin Makarantun Islamiyya da na Allo da su gudanar da wannan taro cikin nutsuwa da kaskantar da kai ga Allah Subhanahu Wata’ala tare da yi masa godiya bisa falalarsa da ya kawo mu wannan duniya a cikin zamanin Shugaban Halitta Annabi Muhammadu Sallalahu Alaihi Wa’ahlihi.

Haka kuma Hon. Jamilu Abubakar Dambatta ya ja hankalin Jami’an tsaro da su himmatu ainun wajen baiwa masu wannan biki kulawa ta musamman domin ganin an gudanar da wannan biki cikin lafiya da kwanciyar hankali.

Daga nan Shugaban ya godewa Gwamna Abba Kabir Yusuf bisa ayyana yau Juma’a a matsayin ranar hutu wanda hakan ya ke nuna tsantsar soyyayarsa da kaunarsa ga Annabin Rahama Sallalahu Alaihi Wa’ahlihi Wasallam.

Har ila yau, ya sake junjinawa Gwamnan akan yadda ya ke gudanar da ayyukan raya ƙasa a duk faɗin Jihar nan tare da yin kira ga al’ummar Jihar nan da su cigaba da yiwa Gwamnatin Abba Kabir Yusuf addu’a na musamman domin cigaba da kwararo ribar Damokradiyya a Jihar nan.

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You May Also Like

Lafiya

Daga Dr. Sunusi U. Na’ibi Yadda mutum ke wanke baki da kuma irin burushin da yake amfani da shi suna iya canza lafiyar baki...

Noma da Kiwo

DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA (2) Daga Yazid Sunusi YahayaRead also: DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA UKU (3)...

Noma da Kiwo

Dabarun kiwan kaji a lokacin yanayi na sanyi Daga Yazid Sunusi YahayaRead also: DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA UKU (3) Sau...

Kano

Gwamnatin Kano Ta ƘirƘiri Sabon Tsarin Biyan Fansho da Giratuti Ta Intanet Gwamnatin Jihar Kano ta ƙaddamar da wani sabon tsari na musamman na...