Connect with us

Hi, what are you looking for?

Ilimi

ASUU Ta Janye Yajin Aiki, Bayan Gwamnatin Tarayya Ta Biya Buƙatar Su

ASSU
ASSU

ASUU Ta Janye Yajin Aiki, Bayan Gwamnatin Tarayya Ta Biya Buƙatar Su

Daga Sunusi K/Na’isa

Ƙungiyar Malaman Jami’o’i ta Ƙasa (ASUU), ta janye yajin aikin da ta fara bayan da gwamnatin tarayya ta biya albashin mambobinta na watan Yunin 2025.

Shugaban ASUU na Jami’ar Abuja, Dr. Sylvanus Ugoh, ya shaida wa Jaridar LEADERSHIP a ranar Talata cewa ƙungiyar ta yanke shawarar janye yajin aikin ne bayan da aka fara biyan mambobinta albashin watan Yuni.

Ya ce, “Albashin Yuni na mambobinmu ya fara shigowa kafin wa’adin da muka bayar ya cika. Saboda haka, ƙungiyar ta dakatar da yajin aikin da ta fara.”

Matashi Mai Shekara 24 Ya Kashe Mahaifinsa A Bauchi

Wannan matakin ya hana yiwuwar rufe jami’o’i a faɗin ƙasar nan.

Tun da farko, shugabancin ASUU na ƙasa ya umarci rassanta da su dakatar da aiki idan aka ƙi biyan albashin Yuni a kan lokaci.

Wannan matakin ya biyo bayan shawarar Kwamitin Zartarwa na Ƙasa (NEC) na ASUU wanda ya amince da tsarin “Ba Albashi, Ba Aiki” saboda yawan jinkirin biyan albashi da suke fuskanta.

ASUU ta ɗora laifin hakan kan Ofishin Akanta-Janar na Tarayya.

Shugaban ASUU na ƙasa, Farfesa Chris Piwuna, ya bayyana a ranar Litinin cewa gwamnatin na nuna halin ko-in-kula kan batun.

Ya ce duk da yawan ganawa da jami’an gwamnati, malamai na fuskantar jinkirin albashi ba tare da wani dalili ba.

“Muna so mu yi aiki, amma ba za mu iya ba saboda ba su ba mu damar yin haka ba. Wannan matsala ce da aka ƙirƙira da gangan. Matsalar ba daga wajen tsarin biyan albashi ba ne, matsalar tana wajen mutanen da ke da alhakin sakin kuɗin ne,” in ji Piwuna.

Tsohon ma’aikacin gidan rediyo Kano, Malam Ali Sufi Utai, ya rasu

Ya ƙara da cewa sauyi tsarin biyan albashi daga IPPIS zuwa GIFMIS ya ƙara jefa malamai cikin wahala.

ASUU ta ce duk wata Jami’a da ba a biya malamanta albashin Yuni kafin 7 ga Yuli ba, to, ya kamata su fara yajin aiki nan take.

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You May Also Like

Lafiya

Daga Dr. Sunusi U. Na’ibi Yadda mutum ke wanke baki da kuma irin burushin da yake amfani da shi suna iya canza lafiyar baki...

Noma da Kiwo

DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA (2) Daga Yazid Sunusi YahayaRead also: DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA UKU (3)...

Noma da Kiwo

Dabarun kiwan kaji a lokacin yanayi na sanyi Daga Yazid Sunusi YahayaRead also: DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA UKU (3) Sau...

Kano

Gwamnatin Kano Ta ƘirƘiri Sabon Tsarin Biyan Fansho da Giratuti Ta Intanet Gwamnatin Jihar Kano ta ƙaddamar da wani sabon tsari na musamman na...