Connect with us

Hi, what are you looking for?

Tsaro

Gwamnan jihar Edo, Monday Okpebholo ya kai ziyarar ta’aziya ga gwamnatin Kano da iyalan mafarauta 16 da aka halaka

Gwamna Kano Abba Yusuf ya karbi ziyarar ta'aziya daga gwamna Edo
Gwamna Kano Abba Yusuf ya karbi ziyarar ta'aziya daga gwamna Edo

Gwamnan jihar Edo, Monday Okpebholo ya kai ziyarar jaje ga gwamnati Kano da iyalan mafarauta 16 da aka halaka daga cikin 21.

Wanna iftula’i ya jawo tashin-tashina a jihar ta Edo, inda gwamnatin jihar da shugabanin al’umma da sauran mahalkanta sukai ala-wadai da abin da ya faru.

Domin ya nuna damuwarsa da jejeto gami da ta’aziya, gwamna Edo, Monday Okpebholo ya ziyarci Kano domin mika ta’aziya.

A Karanta Wanna:Gwamnatin Kano ta karrama Hazikan Gasar karatun Alkur’ani

Da ya ke jawabi a gidan gwamnatin jihar ta Kano, Okpebholo ya nuna kaɗuwa bisa lamarin, inda ya tabbatar da cewa mutane 14 daga cikin waɗanda su ka aikata kisan gillar sun shiga hannun hukuma kuma za a tabbatar an yi wa iyalan wadanda aka kashe adalci.

A saboda haka, Gwamna na Edo, ya bada jama’ar jihar Kano da gwamnati gami da iyalan wadanda suka rasa rayukan su hakuri ga abin da ya faru.

Shi ma gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf ya yi kira ga gwamnan Edo da ya tabbatar da an hukunta waɗanda ake zargi da aikata wanna aikin dabbantaka.

Gwamna Yusuf ya yi kira ga gwamnatin tarayya da ta baiyana fuskoki da sunayen mutane da aka kama kan kisan gillar, inda ya bukaci gwamnan Edo din da ya tabbatar an biya diyya ga iyalan mamatan.

A Karanta Wanna:Shugaba Tinubu ya ayyana dokar ta-ɓaci a jihar Rivers

Idan za a tuna a kwanana wasu ɓatagari suka farma mafarauta da suka fito daga jihar Rivers zuwa Kano domin su gudanar da shagali Sallah.

Mafarautan sun hadu da ajalisnsu a Uromi cikin jihar EDO, inda zauna gari banzan suka rufar musu da duka daga bisani suka kunawa mutane 16 wuta tare da kone su har lahira.

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Advertisement

Trending

You May Also Like

Lafiya

Daga Dr. Sunusi U. Na’ibi Yadda mutum ke wanke baki da kuma irin burushin da yake amfani da shi suna iya canza lafiyar baki...

Noma da Kiwo

DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA (2) Daga Yazid Sunusi YahayaRead also: DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA UKU (3)...

Noma da Kiwo

Dabarun kiwan kaji a lokacin yanayi na sanyi Daga Yazid Sunusi YahayaRead also: DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA UKU (3) Sau...

Kano

Gwamnatin Kano Ta ƘirƘiri Sabon Tsarin Biyan Fansho da Giratuti Ta Intanet Gwamnatin Jihar Kano ta ƙaddamar da wani sabon tsari na musamman na...