Connect with us

Hi, what are you looking for?

Labarai

Gwamnatin Kano ta karrama Hazikan Gasar karatun Alkur’ani

Gwarazan gasar karatun Alkur'ani na kasa
Gwarazan gasar karatun Alkur'ani na kasa

Gwamnatin Kano ta karrama Hazikan Gasar karatun Alkur’ani tare da basu kujerun aikin Hajji

Daga Sunusi Kofarnaisa

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya karrama gwarazan gasar karatun Alƙur’ani mai girma a fadar gwamnati da ke Kano.

A wata sanarwa da Kakakin gwamnan, Sanusi Bature Dawakin-Tofa ya aikewa manema labarai a jiya Talata, gwamnan ya jaddada aniyar gwamnatin sa wajen ci gaban karatun Alkur’ani mai girma da kuma aiki da shi.

A yayin taron, gwamna Yusuf ya sanar da daukar nauyin karatun gwarazan su biyu, Gwani Sunusi Abubakar mai shekara 17 da Gwana Fatima Abubakar zuwa Jami’ar Al-Azahar da ke Egypt domin ci gaba da neman ilimi mai zurfi.

A Karanta Wanna:Shugaba Tinubu ya ayyana dokar ta-ɓaci a jihar Rivers

Baya ga haka, ya baiwa ko wanen su kujerun aikin Hajji da kyautar filaye da kuma kyautar kuɗaɗe.

Gwarazan ƴan asalin jihar Kano ne, inda Gwani Sunusi Abubakar ya fito daga karamar hukumar Gezawa ya samu nasara a matakin kasa tare da Gwana Fatima Abubakar wadda itama ta samu nasara a matakin kasa.

A Karanta Wanna:Ramadan: Gwamnan Kano ya baiwa kungiyoyin ‘Yan jaridu tallafin shinkafa buhu 450

Sauran wadanda su ka zo na biyu da na uku su ma sun samu kyautar Naira miliyan 1 da kujerar aikin Hajji ko wannensu.

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You May Also Like

Lafiya

Daga Dr. Sunusi U. Na’ibi Yadda mutum ke wanke baki da kuma irin burushin da yake amfani da shi suna iya canza lafiyar baki...

Noma da Kiwo

DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA (2) Daga Yazid Sunusi YahayaRead also: DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA UKU (3)...

Noma da Kiwo

Dabarun kiwan kaji a lokacin yanayi na sanyi Daga Yazid Sunusi YahayaRead also: DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA UKU (3) Sau...

Kano

Gwamnatin Kano Ta ƘirƘiri Sabon Tsarin Biyan Fansho da Giratuti Ta Intanet Gwamnatin Jihar Kano ta ƙaddamar da wani sabon tsari na musamman na...