Fagge
Daga Tasiri Dalin Duniya
Read also: Karamar Hukumar Bichi Za Ta Gina Wa Dagatanta 44 Sabuwar Fada
An bukaci Dalibai Yan asalin Karamar Hukumar fagge Waɗanda suka samu horo akan tukin Mota a Makarantar horar koyan tuki a Gidan VIO, da Suyi amfani da Kyawawan ka’idojin tuki da suka Samu Horo akansu.
Shugaban Karamar Hukumar fagge Hon Salisu Usuman Masu ne Ya baiyana hakan a yayin ziyarar karfafa gwiywa da ya kaiwa ɗaliban su ashirin da biyar ‘yan asalin Karamar Hukumar ta fagge.
Read also: Daliban Jami’ar Aliko Dangote dake Wudil sun Karrama Shugaban Hukumar Karota
Ka Iya Karanta Wanna:Daukewar Wutar Lantarki ta ‘Yan Dakikoki ta Jawo Biyan Diyar Sama Da Naira Miliyan 375
Shugaban ya kuma bayar da tabbacinsa na kai makamancin ziyarar ga irin waɗana cibiyoyin da ɗaliban yankin ke koyan sana’a domin karfafa musu gwiywa akan abun da suke koya.
Alhaji Salisu Masu ya kara bada tabbacin majalisar sa na ci gaba da bunƙasa koyar da sana’o’i da bayar da ilimi mai inganci ga matasan yankin, ya ce hakan koyi ne da ƙoƙarin gwamnatin Abba Kabir Yusuf na bunƙasa rayuwar ɗan adam.
Hon Salisu Masu Ya bayar da Naira Dubu Dari Biyar da Hamsin 550,000 yayin ziyarar, inda kowanne Dalibi zai amfana da Naira Dubu Ashirin 20,000 inda kuma ya bayar da Naira Dubu Hamsin ga Shuwagabanin gudanarwar makarantar.
Ka Iya Karanta Wanna:Rigakafin Shan-Inna: Dakta Labaran ya Yabi Ƙananan Hukumomin Uku
Shugaban na Fagge yayi musu fatan alkhairi da addu’o’i domin samun albarka a cikin wannan horo da suka dauka.




























