Connect with us

Hi, what are you looking for?

Labarai

Daukewar Wutar Lantarki ta ‘Yan Dakikoki ta Jawo Biyan Diyar Sama Da Naira Miliyan 375

Wutar Lantarki
Wutar Lantarki

Daukewar Wutar Lantarki ta ‘Yan Dakikoki ta Jawo Biyan Diyar …

Daukewar wutar lantarki na ‘yan lokuta ƙalilan ya sa ƙasar Saudi Arabia ta biya mahajanta jihar Kano wandanda suka sauke faradi a shekarar 2023 makkudan kudade sama da miliyan Dubu Dari Uku da Saba’in da Biyar (₦375) diya.

Shugaban Hukumar Jin dalin Alhazzai na Kano, Alh. Laminu Rabi’u Danbappa ya sanar da hakan a lokacin da yake zama na musamman da Ma’aikatar hukumar.

Kamar yadda Jami’en hulda da jama’a na hukumar, Suleman Dederi ya sanar wa kafar yada labarai ta STENTORNEWS Hausa a yau Laraba.

A Iya Karanta Wanna:Alkalai Sun Yi Gidauniya Domin Kubutar Da Matar Aure Dake Tsare A Gidan Yari

Sanarwar ta ce, Shugaba Laminu ya ce Hukumar Saudiyya ta bayar da kuɗi ga Hukumar Jindadin Alhazzai ta Ƙasa Nijeriya (NAHCON), zuwa ga hukumomin kuda da jindadin alhazzai na jihohi, ciki har da jihar Kano. Inda ya ce makudan kudaden an bayar dasu domin a bawa mahajjatan da sukai aikin hajji a shekara ta 2023 a matsayin fansa sanadiyyar daukewar lantarkin na ‘yen dakikoki a Mina.

Babban Darakta Laminu Danbappa ya kara da cewa adadin kason mahajjatan Kano ya kai jimilar Naira Miliyan Dubu Dari Uku da Saba’in da Biyar da Dari Uku da Chasa’en da Bakwai da Dari Shida da Tamanin (N375,397,680), a inda ko wane mahajjaci zai samu kason Naira dubu sittin da ɗaya da Naira tamanin (₦61,080).

Jaridar STENTORNEWS Hausa, ta ji ra’ayin wasu mazauna jihar Kano ko hukumar wutar lantarki ta KEDCO tana biyan su ‘yan dakikoki ko kwanuka da aka gaza basu hasken wutar lantarki a Najeriya?

A Iya Karanta Wanna:Najeriya ta Samu Tallafin Yuro Miliyan 18 daga EU da Ƙasar Jamus

Malam Garba dake unguwar Gandun Albasa ya ce shi a tsawon shekarun sa 36, bai taba ganin ranar da hukumar lantarki ta bawa abokan huldar su hakuri ba don sun hana su wutar lantarki, ballantana a ce ga wata rana da za a basu wasu kuɗade sanadiyar hakan.

Shi kuwa Muhammad Sani, cewa yayi wanna ba abun mamaki ba ne duba da ƙasar da ta biya diyyar, domin alama ce ta adalen shugabanni. “Ai wata miyar sai a makota”, inji Sani.

A Iya Karanta Wanna:Kwan- Gaba Kwan-Baya: Arewa Baza Ta fita Daga Duhu Ba Sai Nan Da Sati 2 – Inji Minista

Hajiya Hauwa Inuwa ta ce “Garin dali na nesa”, Najiriya, hhhhm! sai dai a zo maka da dogon tsani a ce za a yanke wayar gidanka don baka biya ba, kuma ko da sau biyu aka ba da wutar a wata kuwa. Allah ya kyauta.

← Back

Thank you for your response. ✨

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You May Also Like

Lafiya

Daga Dr. Sunusi U. Na’ibi Yadda mutum ke wanke baki da kuma irin burushin da yake amfani da shi suna iya canza lafiyar baki...

Noma da Kiwo

DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA (2) Daga Yazid Sunusi YahayaRead also: DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA UKU (3)...

Noma da Kiwo

Dabarun kiwan kaji a lokacin yanayi na sanyi Daga Yazid Sunusi YahayaRead also: DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA UKU (3) Sau...

Kano

Gwamnatin Kano Ta ƘirƘiri Sabon Tsarin Biyan Fansho da Giratuti Ta Intanet Gwamnatin Jihar Kano ta ƙaddamar da wani sabon tsari na musamman na...