KNUPDA, ta kaddamar da kwamitin karbar korafi Game da Mallakar Fili da Makamantasu
Hukumar Tsara Birane ta jihar Kano ta kaddamar da kwamitin da zai fara karbar koken-koken masu korafi dangane da mallakar filaye da gidaje da gonaki har ma da shaguna a fadin Jaihar nan
Read also: Kwamitin Binciken Hukumar KNUPDA ya Buɗe Kofar Karɓar Korafe-korafe Ko Shawara Game da Hukumar
Shugaban Hukumar Arc. Ibrahim Yakubu Adamu ne ya sanar da haka a lokacin da ya ke kaddamar da kwamitin mai mutane biyar karkashin jagorancin Daraktan Mulki na Hukumar Alh Aminu Umar.
Kamar yadda Jami’ar Hulda da jama’a ta Hukumar Tsara Birane ta jihar Kano (KNUPDA) Bahijja Malam Kabara ta raba wa manema labarai sanarwar.
Zaka iya karanta wanna:
Read also: Kano: An Soke Dokar Da Ta Kafa Hukumar KNUPDA – Majalisar Dokoki
Shugaban Hukumar yace sun lura da cewa abokan huldarsu na kokawa dangane da yadda wasu daga cikin Jami’an hukumar ke amfani da damar da suke da ita tare da yin-sama-da-fadi da sunan hukumar inda su ke aikata ba dai dai ba
Yace kwamitin zai dinga karbar korafe-korafen al’umma a ranakun Litinin zuwa Juma’a, kuma duk wanda aka samu da laifi zai girbi abinda ya shuka bisa tanade tanaden doka.
Read also: “Babu Wani Dalilin da Zai Sa Na Yi APC”, Wanna Wasan Fulani Ne da Kanuri – Sule Lamido
Da ya ke Jawabi, shugaban kwamitin Alh Aminu Umar yasha alwashin yin aiki tukuru don magance matsalar da hukumar ke fuskanta, yana mai karin haske da cewar zasu dauki mataki nan take ga duk wadanda suka samu da laifi, tare da gabatarwa Hukumar kundin korafe-korafen da suka karba duk bayan watani shida.
Zaka iya karanta wanna:
‘Yan kwamitin sun hadar da Aminu Umar a matsayin Shugaba, da Mujtaba Inuwa da Kabiru Musa Dagumawa da Sani Salisu Kabara sai Abubakar Bala a matsayin magatakardar kwamitin.




























