Daga Farouk Isa Musa
An yi kira ga matasa a jihar nan, musamman wanda suka kamalla makaranta kuma ba su sami aiki ba, da su rungumi sana’o’i don kaucewa zaman-kashe-wando,
Darakta-Janar na Hukumar Samar da Magunguna da Kayan Asibiti ta Jihar Kano, Famasist Gali Sule ne ya yi wannan kira a lokacin da yake jawabi a wurin bikin cika shekara 10 da kammala makaranta da Kungiyar Tsofaffin Daliban Makarantun Sikandiren Kimiyya ta Jihar Kano (KASSOSA) reshen Makarantar Kimiyya da ke garin Dawakin Kudu Aji Na shekarar 2014 (Class 2014) suka shirya a Lahadin nan.
Darakta-Janar din ya ce saboda matsin tattlin arziki da ake fama da shi a kasan nan, da kuma durkushewar masana’antu da kamfanoni, wanda hakan ya jawo karuwar rashin aikin yi, zai fi kyautuwa matasa su kama sana’a don rufawa kansu asiri.
Read also: Makarantar Zam-Zam International ta Yaye Ɗalibai 28 Mahaddata Al-Qur’ani, Ciki Har da Asiya Usman
Famasist Gali Sule ya kara da cewa gwamnatin jihar Kano, karkashin jagorancin Gwamna Abba Kabir Yusuf, tana iya bakin kokarinta don samar wa da jama’a abun yi, ta hanyar ba da jari ga dumbin matasa maza da mata, da kuma gina wuraren koyar da sana’o’i guda 10, da kuma gyarawa tare da bude wadanda suka lalace.
Daga nan sai ya yabawa Kungiyar KASSOSA karkashi Shugabanta na Kasa, Alh. Balarabe Nuhu Jallah, bisa koyar da sana’o’i ga ‘yan kungiyar da ba su sami aiki ba, da kuma ba su jari don dogaro da kai
Har ila yau, Darakta-Janar na DMCSA din ya yi kira ga sauran rasan kungiyar tsofaffin daliban da su yi koyi da uwar kungiyar ta kasa wajan koyawa mambobinsu sana’o’i da ba su jari.
Read also: JAMB ta Dakatar Da Karatun Digirin Haɗaka Tsakanin Jam’i’o’i da Kwalejojin Ilimi A Najeriya
Shugaban kungiyar ta KASSOSA Aji Na 2014, Mal. Abubakar Idris Yarima ya godewa bakin da suka sami damar halartar taron duk da irin hidindumu da ke gabansu.



























