Daga Wakilinmu
Alƙalin Babbar kotun tarayya da ke jihar Kano AM Liman, ya sanya ranar Alhamis, 13 ga watan Yuni domin bayyana matsayar hukuncin kotun na hurumin sauraron ƙarar da aka shigar gabanta kan rushe masarautu biyar a jihar ko kuma rashin hurumin hakan.
Read also: Kotun Kano Ta Yanke Wa Mutum Biyu Hukuncin Kisa Sau Bakwai Kowanne Saboda Kashe Mace Da Yara Shida
Tun da farko kotun ta bukaci bangarorin biyu su yi mata bayani kan ko tana da hurumin ko kuma a’a inda kowanne bangare ya yi bayani tare da kafa hujjoji da irin shari’o’in da suka gabata kan rikicin masarautu a ƙasar.
Read also: Kotu Ta Daure Wani Mutum Wata 3 A Gidan Gyaran Hali Sakamakon Kona Taya A Kano
Lauyan ɓangaren gwamnatin Kano ya shaida wa kotun cewa wanda ya shigar da karar ma ba shi da hurumin neman kare masa hakki saboda dokar da ta ba shi damar zama ɗan majalisar sarki an rushe ta.
To amma lauyan mai ƙara ya ƙalubalanci hakan da cewa, idan ana batu na take haƙƙin ɗan’Adam to al’amari ne da ba shi da iyaka don haka kotun ta ci gaba da sauraron wannan Shari’a.
Read also: Kotu Ta Tabbatarwa ICPC Damar Bincikar Zargin Badaƙalar Tallafin Karatu A Kano
Bayan sauraren doguwar mahawarar daga dukkanin ɓangarori biyun, Alƙalin kotun AM Liman, ya sanar da ranar Alhamis 13 ga Yuni na wanna shekarar, kotun za ta yanke hukunci kan wannan dambarwa.




























