Connect with us

Hi, what are you looking for?

Labarai

Ramadan: Kungiyar HONIA ta Rabawa Marayu Kayan Abinci Da Na Sawa

HONIA
HONIA

Daga Wakilinmu

Ƙungiyar ci gaban unguwar Hotoro a yankin Ƙaramar Hukumar Nassarawa wato HONIA ta tallafawa marayu da gajiyayyu da kayan abinci da kuma Kayan sawa domin rage musu raɗaɗin halin da ake ciki na matsin rayuwa da kuma shirin Sallah ƙarama.

Da yake ƙaddamar da rabon kayan, shugaban ƙungiyar Malam Muhammad Kabir Usman ya ce tallafin wanda aka dauki tsawon lokaci ana yinsa yana mayar da hankali domin tallafawa marayu da gajiyayyu a cikin al’umma musamman a watan Ramadan.

Ya ce an tallafawa marayu da gajiyayyun su goma 10 da taliya Katan ɗai-ɗai da atamfofi ko yaduka kowannensu domin gudanar da azumin watan Ramadan da bukukuwan Sallah cikin farin ciki da annashuwa.

A Karanta Wanna: Gwamnatin Kano ta yi Tur da Yadda Ake Rabon Abincin Watan Azumi

“Mun a raba wadannan kayayyaki ne ƙarƙashin jagorancin wannan kungiya ta HONIA wacce take a Kan layin Garsan Fulani a unguwar Hotoron Arewa, wannan tallafi an same shi ne daga gudun mowar da al’ummar wannan unguwa suka bayar Allah ya saka musu da alkhairi, dama anayi a baya, a wannan karon an sake bijoro da shi ne sakamakon matsin rayuwa da al’umma suka sami kansu a ciki,” inji Malam Kabir.

Daga nan ya yabawa al’ummar da suka bada gudun mowar tare da kwamitin da aka naɗa wanda ya karbo tallafin don rabawa mabuƙata.

A nasa ɓangaren shugaban Kwamitin karbo tallafin Alhaji Sanusi Malumfashi ya ce dama an samar da kwamitin ne domin karbo tallafin daga Mawadatan dake tsakanin al’umma a unguwar don bawa marayu da kuma gajiyayyu.

A Karanta Wanna: Ɓarayi Sun Wawashe Kayyan Taransifoma Na Sama Da Naira Miliyan Ɗaya Da Rabi A Ɗiso

Sanusi Malumfashi ya buƙaci shugabanni da mawadata da gwamnatoci da su riƙa tallafawa na mabuƙata, musamman a watan Ramadan don samun falala a gurin Allah.

Da suke karbar tallafin, Iyalan Marigayi Malam Sabo Direba sun bayyana farin cikinsu tare da yaba wa ƙungiyar ta HONIA bisa kula da su bayan rasuwar mahaifinsu.

← Back

Thank you for your response. ✨

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Advertisement

Trending

You May Also Like

Lafiya

Daga Dr. Sunusi U. Na’ibi Yadda mutum ke wanke baki da kuma irin burushin da yake amfani da shi suna iya canza lafiyar baki...

Noma da Kiwo

DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA (2) Daga Yazid Sunusi YahayaRead also: DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA UKU (3)...

Noma da Kiwo

Dabarun kiwan kaji a lokacin yanayi na sanyi Daga Yazid Sunusi YahayaRead also: DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA UKU (3) Sau...

Kano

Gwamnatin Kano Ta ƘirƘiri Sabon Tsarin Biyan Fansho da Giratuti Ta Intanet Gwamnatin Jihar Kano ta ƙaddamar da wani sabon tsari na musamman na...