….Ana ta zanga-zanga a ginin majalisar dokokin Amurka kan kin kudurin
Shugaban kamfanin shafin sada zumunta da muhawara na TikTok ya ce, kamfanin zai yi duk abin da zai iya domin kare kansa, bayan da majalisar wakilan Amurka ta amince da wani ƙudurin doka, da zai iya kaiwa ga haramta amfani da shafin a Amurka.
Read also: Ingila Za Ta Haramta wa Dalibai Amfani da Wayoyin Hannu a Makarantu
Fadar Gwamnatin Amurka, White House, ta yi kira ga ‘yan majalisar dattawa da su gaggauta amincewa da ƙudurin, wanda ‘yan majalisa suka ce zai kare Amurkawa daga barazanar alaƙar TikTok ɗin da gwamnatin China.A wani hoton bidiyo da ya sanya a shafin na TikTok, shugaban kamfanin Shou Zi Chew ya yi gargaɗin cewa muddin aka zartar da wannan doka, to dokar za ta kai ga hana amfani da shafin gaba ɗaya a Amurka.
Ka karanta Wanna: Shaharrariyar Ƴar Tiktok Murja Kunya Ta Faɗa Komar Hisbah A Kano
A don haka ya ce, kamfanin zai yi amfani da dama da ‘yancin da yake da shi na doka ya kare shafin da kuma Amurkawa miliyan 170 da suke amfani da shi.
Mista Chew ya ce manufar matakin kawai haramta amfani da manhajar ne.
Read also: Shugaban ‘Yan Bindiga Bello Turji Na yunƙurin Miƙa Wuya Bayan Mutuwar Yelo Danbokolo
Ya ce : ”Wannan dokar, idan aka amince da ita za ta kai ga hana amfani da TikTok ne a Amurka. Hatta ma waɗanda suka kawo ƙudurin sun yadda cewa burinsu kenan. Wannan kudurin doka ya bayar da ƙarin iko ga wasu kamfanonin shafukan sada zumunta da muhawara ‘yan kaɗan. Haka kuma zai raba masu ƙirƙira da masu ƙananan harkokin kasuwanci biliyoyin dola. Zai kuma jefa aikin Amurkawa sama da dubu 300 cikin haɗari, kuma zai ɗauke TikTok ɗinku.”
Ka karanta Wanna: Ƴar Tik Tok Ta Yi Ɓatan Dabo: Al’ummar Kano Na Ce-Ce-Kuce Kan Sharuɗɗan Beli
Fadar gwamnatin Amurka, White House ta ce tana goyon bayan ƙudurin dokar, da zai bai wa masu shafin ‘yan China damar kusan wata shida ta ko dai su sayar da shafin ko kuma su fuskanci haramcin amfani da shi a wayoyi.
‘Yan majalisar na ɗaukar shafin a matsayin wata barzana ga tsaron Amurka.
Kamfanin na TikTok ya musanta alaƙa da gwamnatin China, ya kuma buƙaci masu amfani da shafin a Amurka, da su yi ta kiran wayoyin ‘yan majalisar, su buƙace su da su yi watsi da wannan doka.
(BBC)



























