Connect with us

Hi, what are you looking for?

Labarai

“Da Akwai Alaƙa Ta Kusa Tsakani Ɗabi’ar Mutane Da Ci gaban Ƙasa”,- Dr. Ƙofarmata

Dr Kofarmata
Dr Kofarmata

Daga Wakilinmu

Kwamishina Ma’ikatar ilimi mai zurfi, Dakta Yusuf Ƙofarmata ya ce sai ɗan adam ya zama mutumin kirki a ɗabi’arsa da neman iliminsa a makarantar boko ko ta Muhammadiyya da ɗaukacin ayyukansa shi yake bayuwa a sami mutun na gari daga nan sai a samu al’umma mai inganci sanan a samar da ci gaban ƙasa mai ɗorewa.

” Wannan shine tsarinmu a Kwankwasiyya kuma tarbiyar Jagoranmu, don haka ya samar da makarantu masu yawa waɗanda suka haɗar da na Sakandare, da na koyan sana’a da kuma jami’oi domin horas da tarbiya da kuma bayar da ilimi mai iganci”. Inji Kofarmata.

Kwamishina ya furta haka ne da yake jawabi a madadin Mataimakin gwamna Kano, Kwamared Aminu Abdulsalam Gwarzo a bikin buɗe babban taron ƙarawa juna sani na ƙasa, wanda aka gudanar a Jami’ar Yusuf Maitama Sule, karo na uku. Mai taken ” Ɗabi’ar Ɗan Adam da Ci gaban Kasa”, wanda jami’ar ta shirya a ƙarƙashin Tsangayar Nazarin Halayar Ɗabi’ar ɗan adam, a yau Litini.

Ya ce lashaka, kyakyawar ɗabi’a tana da alaƙa ta kusa da bunƙasar ci gaban ƙasa, inda ya ce shine muradden gwamnatin Abba Kabir Yusuf. Ya bada tabbacin gwawamnati na ci gaba da horas da matasa kyawawan ɗabi’u, musamman ɗalubai wanda ƙasa ke alfahari dasu domin samun shugabani masu nagarta a nan gaba.

Dokta Ƙofarmata ya gode wa mahalarta taron waɗanda suka fito daga jihohi daban-dabam da kuma ɗaluban jami’ar da waɗanda suka gabatar da muƙala da shgabanin da suka haɗarci taron da kuma Tsangayar nazarin ɗabi’a na jami’ar.

Farafesa Abdullah Uba Adamu da Farfesa Kamilu Sani Fagge na daga cikin waɗanda suka bayar da Muƙala a gun taron. Sarkin Shanun Kano, Alh. Shehu Muhammad Ɗankade shi ya jagoranci taron.

1 Comment

1 Comment

  1. Pingback: Gwamnatin Kano Zata Biyama Ɗaliban Manyan Makarantu 24,651 Kuɗin Makaranta A Karo Na Biyu - The StentorNews Hausa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You May Also Like

Lafiya

Daga Dr. Sunusi U. Na’ibi Yadda mutum ke wanke baki da kuma irin burushin da yake amfani da shi suna iya canza lafiyar baki...

Noma da Kiwo

DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA (2) Daga Yazid Sunusi YahayaRead also: DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA UKU (3)...

Noma da Kiwo

Dabarun kiwan kaji a lokacin yanayi na sanyi Daga Yazid Sunusi YahayaRead also: DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA UKU (3) Sau...

Kano

Gwamnatin Kano Ta ƘirƘiri Sabon Tsarin Biyan Fansho da Giratuti Ta Intanet Gwamnatin Jihar Kano ta ƙaddamar da wani sabon tsari na musamman na...